Bisa kuskure jirgin yaki ya kashe fararen hula a Yobe - Rundunar Sojin Najeriya

Nig Airforce

Asalin hoton, Nig Airforce

An wallafa

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce a bisa kuskure ne jirgin sojinta ya kai hari tare da kashe fararen hula a garin Buhari da ke karamar hukumar Yunusarin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Shaidu sun ce harin jirgin saman na ranar Laraba ya yi sanadin kashe aƙalla mutum goma, baya ga gommai da suka jikkata cikinsu har da mata da ƙananan yara.

Da farko dai rundunar sojin ta musanta faruwar lamarin, amma a ranar Alhamis ta fitar da wata sanarwa tana bayyana kuskuren da ya faru har aka samu wannan hatsari.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran rundunar sojin saman Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce jiragen sojin na shawagi ne yankin Kogin Kamadougou Yobe don tattara bayanan sirri kan ayyukan kungiyoyin Boko Hraam da ISWAP.

"Rundunar Operation Hadin Kai ta samu bayanan cewa ana aikata ayyukan ta'addanci a kan iyakar Najeriya da Nijar da misalin karfe 6 na safe ranar 15 ga watan Satumban 2021".

"A yayin da jirgin yake aiki a Kudancin Kanama sai ya gano wani shige da fice da bai yarda da shi ba da yake da alaka da ayyukan 'yan ta'addan Boko Haram a duk sanda jirgin ke shawagi.

"Daga nan sai matukin jirgin ya bude wuta. Amma yana da muhimmancin a gane cewa dama yankin ya yi kaurin suna da ayyukan Boko Haram da ISWAP.

"Sai dai abin bakin ciki rahotannin da muke samu a yanzu sun nuna cewa ana zargin jirgin ya kashe fararen hula da jikkata da dama," in ji sanarwar.

Rundunar ta ce rahoton farko da ya karyata hatsarin ya ta'allaka ne a kan bayanan farko da rundunar sojin saman ta samu, wanda ke cewa jirgin yakin ya jefa bama-bamai ne a kan fararen hula.

A yanzu dai ta ce na kafa kwamitin bincike kan abin da ya haddasa lamarin.

'Yan uwana takwas harin jirgin soji na Yobe ya shafa'

Wani mutum da lamarin ya yi sanadin mutuwar danginsa takwas ya ce jirgin yaƙin ya harba makami fiye ɗaya a kan gidajen mutane.

Ya kara da cewa wadanda lamarin ya shafa ko dai su na shirin zuwa kasuwa ne, ko gona ko wadanda ke zaune a cikin gida su na gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

''Jirgin ya zo daga gabas ya na ta barin wuta sai kuma ya yi yamma, daga nan sai ya yi kudu ya na ta zuba wuta babu kakkautawa. Lamarin ya shafi kanin babana, akwai kakana da matar babana da sauran yaransu kanana, 'yan uwana kadai sun kai takwas. Mun kawo su asibiti cikin gaggawa, ana yi musu magani ,wadanda suka mutu kuma an binne su. Mun je mun kai rahoto ga shugaban karamar hukumarmu kuma sun kawo ma na taimakon gaggawa,'' inji Alhaji Ali Lawan.

Alhaji Ali, ya ce lamarin ya faru ne da safe kowa ya na gani, kuma sun tabbatar da cewa jirgin sojoji ne saboda ya yi kasa-kasa sannan mutane sun gan shi da idonsu, an kuma cire wa wadanda abin ya shafa albarusai da karafa. Sannan mutane na fadin launin fentin jirgin irin na kakin soji ne, wasu na cewa launin ruwan toka ne.

Ya ce,''Wadanda suka ji munanan raunuka ni da kai na ne na yanka musu takardar asibiti su 20, kuma yara kananan da suka ji ciwo aka za a wuce da su babban asibiti da ke Maiduguri. Yayin da wadanda suka rasu kuma mutum takwas.''

Daga bisani daya daga cikin jiragen ya yi aman wuta kan wani bangaren garin, kamar yadda wani da 'yan uwansa suka mutu a lamarin ya shaida wa BBC.

BBC ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Yobe inda kakakinta ASP Dungus Abdurrahman, ya ce ba su samu labarin ba, amma za su tuntubi BBC idan suka samu labarin.

Sai dai kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya musanta yin ɓarin wuta a cikin wata sanarwa da ya fitar.

"Rundunar sojin sama ta gudanar da aikinta na karshe a jihar Yobe (ba a karamar hukumar Yunusari ba) a ranar 5 ga watan Satumban 2021, kuma bincike aka yi ya nuna cewa ba a saki bam ko makami mai linzami ba," in ji sanarwar.