Amurka da kasashen Turai sun bullo da sabon shirin tsaron da China ke adawa da shi

Amurka da Birtaniya da kuma Australia sun sanar da wani sabon shiri kan harkokin tsaro a yankin Asiya lamarin da ya janyo mummunar suka daga China.
A cikin yarjejeniyar za a samar da jiragen ruwa masu aiki da nukiliya ga sojoji ruwan Australia, wadannan jiragen ruwa dai za su rinka dauko makaman da aka saba amfani da su.
China ta yi kakkausar suka kan wani sabon kawancen tsakanin kasashen inda ofishin jakadancin kasar a Amurka ya zargi kasashen da ra'ayin yakin cacar baka.
To amma a wani taron manema labarai da aka yi a Canberra, firaministan Australia, Scott Morrison, ya kare yarjejeniyar.
Wannan sanarwa ta sabon shiri kan harkokin tsaron dai na nufin Australia ta janye shirinta na sayan sabbin jragen ruwa daga Faransa.

Scott Morrison ya yi Karin haske game da wannan sauyi da suka yi.
"Ya ce wannan wani shiri ne na musamman kuma mai matukar muhimmanci ga Australia. A shekarar 2016 da aka dauki wannan mataki na samar da jiragen masu aiki da nukiliya, Australia ba ta da wannan karfi, kuma a wancan lokacin babu wannan shiri saboda dalilai da dama".
Firaministan ya kara da cewa, burinsu bai sauyawa ba, kuma yan kasar Australia za su tabbatar cewa shi a matsayinsa na firaminista zai tabatar da zaman lafiyarsu.











