Ana zargin malamin makaranta da sanya wa ɗalibansa cutar HIV a Neja

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Neja a arewacin Najeriya ta sanar da kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan zargin fyde da ake yi wa wani malamin makarantar firamare.
Ana zargi malamin na makarantar firamaren garin Karabonde cikin karamar hukumar Bargu a jihar Neja da lalata yara 14 abin da ya sa ake fargabar sun harbu da cuta ƙwayar cutar HIV.
Hukumar kula da ilimin bai-ɗaya a jihar Neja ta ce ta dakatar da malamin har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ɗaliban suna asibiti ana duba su.
Wani mutumin garin Karanbonde ya ce suna jiran sakamakon bincken likitoci domin tabbatar da ko ɗaliban na ɗauke da ƙwayar cutar HIV.
Kwamishinar ilimi ta Neja Hajiya Hannatu Jibrin Salihu ke jagorantar kwamitin binciken lamarin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da daraktan hukumar kare haƙƙin yara da kwamishinar harkokin mata da kuma shugaban hukumar kula da ilimi bai daya.
Yanzu haka dai wanda ake zargin yana hannu ƴan sanda inda suke gudanar da bincike.
Bayanai na cewa nan gaba kaɗan, za a mika malamin da ake zargi da lalata yaran, ga kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa don ci gaba da bincike da zaran hukumar binciken ƴan sanda ta kammala nata binciken.











