Zaɓen ƙananan hukumomi: Jam'iyyun siyasa a Kaduna sun cimma yarjejeniya

An wallafa

Jam'iyyun siyasa a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya sun cimma yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu yayin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar ranar Asabar mai zuwa.

Jam'iyyun sun cimma wannan yarjejeniya ne a yayin wani taro da suka gudanar a jihar ta Kaduna.

Rundunar yan sandan jihar ta Kaduna ce ta shirya wannan taron wanda ya samu halarcin wakilai daga jam'iyyun siyasa daban-daban da masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa shirya irin wannan taron ya zama wajibi musamman idan aka yi la'akari da yadda a baya zaɓukan kan bar baya da ƙura.

A cewar rundanar, taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi domin ganin an gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi cikin kwanciyar hankali.

ASP Muhammad Jalige, shi ne kakakin ƴan sandan jihar Kadunan, kuma ya shaida wa BBC cewa duka jam'iyyun siyasar da za su shiga zaben sun saka hannu kan wannan yarjejeniya kan sharaɗin cewa za a zauna lafiya ba tare da tsangwama ba ko tayar da zaune tsaye.

"Jami'anmu suna nan za su yi aiki kamar yadda ya kamata domin tabbatar da cewa wanda jama'a suka zaɓa an tabbatar da shi a matsayin wanda ya ci zaɓe

Jam'iyyun siyasar APC da PDP ne kan gaba a wannan yarjejeniyar.

Honorabul Yahaya Baba Pate, shi ne sakataren Jam'iyyar APC na jihar Kaduna, kuma ya shaida wa BBC cewa jam'iyyar APC ta yi wa jama'ar jihar Kaduna alƙwarin cewa za ta tabbatar da zaman lafiya.

"Mun yi wa jama'ar jihar Kaduna alƙawarin cewa idan Allah ya so ya yarda, da mu da magoya bayanmu kamar yadda aka sanmu, za mu yi ƙoƙari a zauna lafiya, kafin zaɓe da lokacin zaɓe da bayan zaɓe," in ji Yahaya Pate.

Sai dai a nata ɓangaren, babbar jam'iyar adawa ta PDP a jihar Kadunan ta ce duk da cewa ta saka hannu a yarjejeniyar, ta yi haka ne bisa wasu sharuɗa inda ta ce ba za ta sake zura ido ba a yi mata sakiyar da ba ruwa.

Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono, shi ne sakataren jam'iyyar PDP na jihar ta Kaduna, kuma ya shaida wa BBC cewa PDP mutane ne masu son zaman lafiya sakamakon duk inda ake tayar da hatsaniya babu hannun PDP.

"Abubuwan da suka faru, mun ji mun yarda mun saka hannu amma bisa sharuɗa kuma sharuɗan sun hada da abin da ya faru a zaɓen 2018 kada ya sake faruwa," in ji Alhaji Wusono.

Ko da BBC ta tambaye shi irin abubuwan da suka faru sai ya ce "Abin da ya faru shi ne ƙananan hukumomi kusan goma sha uku an gama zaɓe kuma ba malaman zaɓen da za su sanar da zaɓe, kawai sun yi ɓatan dabo."

A cewarsa, waɗanda yake zargi da aikata hakan sun sake ikirarin yin haka wanda hakan ya sa suka miƙa wa kwamishinan ƴan sandan jihar wani bidiyo na ikirarin waɗanda suke zargin a matsayin hujja.

A yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar ta Kaduna ta ce ta tuni aka tanadi jami'an tsaro kimanin dubu goma sha daya, domin samar da tsaro a lokacin zaɓen ƙananan hukumomin.