Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sako ɗalibai 32 na sakandaren Bethel Baptist ta Kaduna
Rahotanni na cewa 'yan bindiga sun saki ƙarin dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist da ke Jihar Kaduna.
Wani mahaifi da BBC Hausa ta zanta da shi ya ce sun karɓo ya'yan nasu bayan biyan kudin fansa, amma har yanzu 'yan bindigar na rike da ƙarin ɗaliban 31.
Ya kuma ce tuni an haɗa daliban da iyayensu.
Sakin daliban Bethel Baptist na zuwa kwana ɗaya bayan sakin ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina a Jihar Naija bayan shafe kwana 88 a hannun 'yan fashin daji.
A ranar 5 ga watan Yuli ne 'yan bindigar suka kutsa makarantar Bethel Baptist da ke kan titin Kafanchan zuwa Kaduna, inda suka sace ɗalibai 121.
'Yan fashin sun sako 28 daga cikinsu a ranar 25 ga Yuli bayan an biya kuɗin fansa.
Kazalika, sun sake sako ƙarin 15 a ranar 22 ga Agusta, abin da ya kawo adadin waɗanda suka kuɓuta zuwa 90.