Hotunan Afirka na mako 13-19 Agustan 2021: Masu shigar Ninja, wutar daji da ganguna

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga sassan Afirka na wasu abubuwan da suka faru a nahiyar a wancan makon, ku kuma na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya.

Short presentational grey line
Wata tawagar ƴan fareti a bikin cikar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika shekara 61 da samun ƴanci a Camp Kasai a Bangui ranar Juma'a Agusta 13, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata tawagar ƴan fareti a bikin cikar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika shekara 61 da samun ƴanci a Camp Kasai a Bangui ranar Juma'a
Ƙungiyar Ƴan Rastafari ranar Talata ta shirya shuka bishiyoyi don tunawa da ranar haihuwar mai fafutukar kare haƙƙin baƙar fata ɗan ƙasar Jamaica, Marcus Garvey

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ƙungiyar Ƴan Rastafari ranar Talata ta shirya shuka bishiyoyi don tunawa da ranar haihuwar mai fafutukar kare haƙƙin baƙar fata ɗan ƙasar Jamaica, Marcus Garvey
A Addis Ababa kuwa wasu ƴan rawa ne suke wasa a wani bikin bankwana da aka shirya wa rundunar sojin Habasha da za su tafi yaƙi Tigray ran 13 ga Agusta 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Addis Ababa kuwa wasu ƴan rawa ne suke wasa a wani bikin bankwana da aka shirya wa rundunar sojin Habasha da za su tafi yaƙi Tigray
A Zambia, magoya bayan jam'iyyar adawa ta United Party for National Development (UNDP) na rawa bayan da aka sanar da Hakainde Hichilema a matsayin wanda ya ci zaɓen ƙasar ranar Litinin ran 16 ga Agustan, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Zambia, magoya bayan jam'iyyar adawa ta United Party for National Development (UNDP) na rawa bayan da aka sanar da Hakainde Hichilema a matsayin wanda ya ci zaɓen ƙasar ranar Litinin
Ɗan wasan dambe na Ghana Samuel Takyi magoya bayansa na barbaɗa masa hoda a lokacin da ya koma gida daga gasar wasanni Olympics a Tokyo inda ya ciwo tagulla ran 13 ga Agustan, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan dambe na Ghana Samuel Takyi magoya bayansa na barbaɗa masa hoda a lokacin da ya koma gida daga gasar wasanni Olympics a Tokyo inda ya ciwo tagulla
Survivor of 1921 Tulsa race massacre, 107 year-old Viola Ford Fetcher holds a bouquet, a gift from Action Chapel International during a church service in Accra, on August 15, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bayan kwana biyu, wata da ta tsira a lokacin kisan gillar Tulsa a shekarar 1921, Viola Ford Fetcher mai shekaru 107 riƙe da furanni a lokacin wani bikin a coci a Accra inda ta ke ziyartar ɗan uwanta...
Hughes Van Ellis mai shekaru 100 wanda shi ma ya tsallake rijiya da baya a gisan gillar. Tsakanin Mayu da Yunin 1921

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, ...Hughes Van Ellis mai shekaru 100 wanda shi ma ya tsallake rijiya da baya a gisan gillar. Tsakanin Mayu da Yunin 1921, wasu gungun fararen fata ta kashe baƙar fata sama da 300 sannan ta lalata sana'o'in baƙaƙen fata a unguwar Greenwood a birnin Tulsa na ƙasar Amurka.
A firebird named Zharishka, the official Mascot of the FIFA Beach Soccer World Cup Russia 2021, welcomes the team of Senegal during a training session

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Laraba, butum-butumin gasar ƙwallon ƙafa na yashi na Fifa Beach Soccer World Cup na 2021 mai suna Zharishka, na yi wa tawagar Senegal maraba lokacin wani atisaye
Cameroonian artist Salatiel performs a song at the opening of the draw ceremony for the 2022 African Cup of Nations (CAN) in Yaounde, Cameroon, on August 17, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Talata a Kamaru, ƴan rawa Salatiel na wasa a lokacin buɗe taron Gasar Cin Kofin Afrika na 2022 (CAN) wanda za a yi a ƙasar
A Moroccan tries to help put out a fire as wild blazes destroyed some 200 hectares (500 acres) of forest in the region of Chefchaouen in northern Morocco on August 15, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum na ƙoƙarin taimaka wa wajen kashe wutar daji a Morocco da ta lalata sama da hekta 200 na daji a yankin Chefchaouen a arewacin ƙasar
A Royal Moroccan Air Force Canadair plane douses a wildfire in the region of Chefchaouen of northern Morocco on August 17, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar talata an kai agaji daga sama a lokacin da jirgin sojin saman Morocco ke kashe wutar
Residents climb to the rooftop to help put out a fire that razed twelve homes in Bombolulu, Kibera

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A rana guda a Kenya, mazauna sun taimaka wajen kashe wutar da ta ƙona gidaje 12 a Bombolulu a Kibera inda mazauna suka kasance babu muhall
Senegal's plastic man Modou Fall, wearing an outfit made of plastic bags, walks around the city to raise awareness on the plastic waste in Dakar, Senegal on August 16, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin, Modou Fall na Senegal, sanye da tufafin da aka yi da jakunkunan leda yana yawo a garin Dakar don wayar da kai al'uma kan munin amfani da ledoji
Abdel Qader Ahmed, a self-taught ninja enthusiast known as Abouda Ninja, holds a sword he made himself, at a field in the Sharqia Governorate, north of Cairo, Egypt August 13, 2021.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Abdel Qader Ahmed wanda aka fi sani da Abouda Ninja, ɗan masar da ya koya wa kansa wasan Ninjatsu na riƙe da takobin da ya ƙera da kansa a wani fili a arewacin Cairo ranar Juma'a

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.