Me ya sa wasu 'ƴan Najeriya ba sa cin moriyar inshorar lafiya?

An wallafa

Wani rahoton masana harkar inshorar lafiya a Najeriya ya ce kusan kashi casa'in na 'yan kasar ba sa cin moriyar tsarin inshorar lafiya na gwamnati da aka fito dashi sama da shekaru 20 da suka wuce.

Rahoton ya ce a tsawon wadannan shekaru kasa da mutun miliyan goma ne kawai ke cin gajiyar shirin, kuma suma ba sa samun ingatacciyar kulawa a asibitocin kasar.

An kafa Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIS ne a shekarar 1999, sai dai tun daga lokacin kawo yanzu, kasa da kashi goma ne kawai na 'ƴan Najeriya- mafi yawansu ma'aikatan gwamnati- ke cin moriyar shirin.

Sai dai rahoton ya zargi ita kanta hukumar da kamfanonin da ke kwangilar haɗa al'uma da asibitoci wato HMO da almundahana.

Hukumar ta NHIS ta sha fuskantar rikicin cikin gida musamman inda aka riƙa zarginta da hada kai da waɗannan kamfanoni wajen aikata cin hanci da rashawa.

Farfesa Muhammad Nasiru Sambo, shugaban hukumar ya ce a baya ya sa wa kamfanonin haɗa al'umma da asibitoci ido amma a ƴan shekarun baya-bayan nan ana ladaftar da su.

"A shekaru baya kafin na shigo hukumar, yawancin asibitoci suna bin waɗannan HMO kudade masu yawan gaske. Amma zuwana , na kafa wani tsari wanda za a tabbatar da duk kamfanonin da asibitoci ke bi bashi sun biya su kuɗinsu.

"Mun sa duk wani asibiti da ke bin waɗannan HMO kuɗi ya sanar da mu. A haka muka gano cewa kudin da ake bin kamfanonin nan sun ka Naira biliyan biyar," a cewar Farfesa Muhammad Nasiru.

Sai dai ya ce kawo yanzu, bayan fara amfani da tsarin nasa mafi yawan kamfanonin sun biya bashin.

Ya kuma ce sun fara ɗaukar mataki kan kamfanonin da suka gaza biyan bashin da ke kansu.

"Akwai kamfanoni guda goma da suka gaza biyan basukansu, yanzu mun cire sunayensu daga rajistarmu," in ji shi.

Ya bayyana cewa a baya ba a soke kamfanonin HMO daga rajistar hukumar NHIS, "sai a bar su suna cin karensu ba babbaka."

Farfesa Sambo ya musanta zargin cewa ana aikata cin hanci da rashawa a cikin hukumar ta NHIS.

Ya ce akwai buƙatar yin garambawul ga dokar da ta kafa NHIS don tilasta duka kamfanoni da ma'aikatu a Najeriya shiga tsarin na inshorar lafiya.

Haka kuma, ya yi bayanin cewa akwai buƙatar samar da hanyoyin agaza wa masu karamin karfi da ba ma'aikatan gwamnati ba, wadanda kuma ba sa iya zuwa asibiti saboda matsalar rashin kuɗi.

Mece ce inshorar lafiya?

Shirin inshorar lafiya kamar wani asusu ko adashi ne, inda mai lafiya zai taimaki marasa lafiya, mai karfi ya taimaki marasa karfi.

Hukumar inshorar lafiya wadda aka kafa tun 1999, na da tsarin cire wani kaso na albashin ma'aikatan gwamnati don sanya wa cikin asusunta ta yadda idan su ko iyalansu ba su da lafiya, za a biya musu kudin magani.

Sai dai, bayan shekaru hukumar ta fahimci cewa ma'aikatan gwamnati su kalilan ne, idan an kwatanta da daukacin al'ummar Nijeriya.

Don haka hukumar inshorar lafiya ta kasa ta bullo da shirye-shirye da dama, don mutanen da ba sai lallai ma'aikatan gwamnati ba su amfana.

Shirin Inshorar lafiya a Najeriya na fuskantar ƙalubale da dama amma babban wanda ta ke fuskanta shi ne karancin masu cin gajiyarsa.