Maganin ƙwari yana matuƙar kashe ƙudan zuma - Bincike

    • Marubuci, Daga Victoria Gill
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent, BBC News
  • An wallafa

Magungunan kwari da ake sayar wa manoma wadanda aka gauraya su suna kashe kudajen zuma har ninki biyu, a cewar wasu sabbin bincike 90 da aka gudanar.

Hakan ya nuna tasirin maganin kwari da rashin isasshen abinci mai gina jiki suke yi a kan muhalli.

Masu binciken sun wannan lamari ya bayyana yadda haduwar wadannan matsaloli take yin tasiri kan yadda kwari suke haihuwa.

Sun ce ya kamata masu sayar da magungunan kwari, wadanda ke dauke da sinadarai daban-daban, suna bukatar yin lasisi.

"Ba wani sabon abu ba ne mu'amala da magungunan kwarai," a cewar Dr Harry Siviter, daga Jami'ar Texas da ke Austin, wanda ya jagoranci binciken, a hirarsa da shirin Inside Science na BBC Radio 4.

Wani bincike da aka fitar a 2016 ya nuna cewa gidajen zuma da aka fesa wa magungunan kwari da yawa sun fi yiwuwar mutuwa.

"Idan aka samu gidan zuma da yake kusa da maganin kwari guda daya hakan zai iya kashe kashi 10 na kudan zuma," a cewar Dr Siviter.

'Karuwar bijirewa'

Wani binciken kuma da aka wallafa a wannan mako, ya nuna cewa kudajen zuma a fadin duniya suna samun wata kariya da ke "kawar" da musamman illar da kwari irin su zago - wadanda ke rayuwa da kuma samun abinci daga jikin kudan zuma - suke da ita.

Tuni dama kudan zuma suke da tsarin tsafta mai sarkakiya, kamar cire kwaikwayen da suka gurbata daga jikinsu.

Yanzu kuma, bayanan da aka wallafa a mujallar in the Royal Society journal Proceedings B, daga binciken da aka kwashe shekara 40 ana yi kan gidajen kudan zuma da suka rayu ba tare da an yi musu feshin maganin kwari ba, sun nuna cewa suna "sauya salo daban-daban" na halayyarsu domin bijirewa zago.

" Muna ganin irin wannan bijirewa tana karuwa a fadin duniya," a cewar Isobel Grindrod, daga Jami'ar Salford.