Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hajj 2021: Hotunan yadda aka gudanar da tsayuwar Arafa a Muna
A ranar Litinin 19 ga watan Yulin 2021 wanda ya yi daidai da 9 ga Zul Hijja ne aka yi tsayuwar Arafa ta bana.
Dubban Musulmai ne suka yi hawan Arfan a Mina, kusa da birnin Makkah na Saudiyya, a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ibadu na aikin Hajji.
Mahajjatan sun shafe sa'o'i da dama a filin na Arfa kuma a filin na Arfa ne Manzon Allah (SWT) ya yi huɗubarsa ta ƙarshe.
Kamar bara, a bana ma kasar Saudiyya ta taƙaita yawan Musulman da za su yi aikin hajjin zuwa mutum 60,000 kuma wadanda dama mazauna kasar ne kawai, a maimakon mutum kusanm muliyan uku da kan yi a duk shekara.
Manufar ita ce takaita yaduwar cutar korona.
Ga wasu zaɓabbun hotuna na yadda tsayuwar Arafan ta kasance.
Dukkan hotunan haƙƙin mallakar Getty IImages da Haramain Sharifain ne.