Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
MDD ta ba da damar ci gaba da kai agaji Syria
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da murya daya a kara tsawon wa'adin aikin agaji, da safarar kayayyakin taimako zuwa cikin Syria daga Turkiyya, da shekara daya.
A yau Asabar ne da lokacin aikin da aka dade ana yi zai kare, to amma ma'aikatan agajin suka yi gargadin cewa halin da ake cikin zai kara tabarbarewa matuka idan aka rufe hanyar iyakar kasashen biyu ta Bab al-Hawa, inda ake bi a kai taimakon.
Nan dai wurin binciken ababan hawa ne na wannan kan iyaka, inda ake bi da kayan abinci da magani da kuma riga-kafi a tsallaka da su daga Turkiyya zuwa Syria, domin kai wa mutane miliyan uku da rabi, wadanda da dama daga cikinsu suna matukar bukatar taimakon domin su rayu.
Suna zaune ne tamkar a tsare a sansanonin wucin-gadi a yankin cikin kasar Syria da ke karkashin ikon 'yan tawaye.
Tun da farko Rasha ta nuna alamun cewa ba ta da niyyar sabunta yarjejeniyar, tare da barin hanyar shigar da kayayyakin agajin a bude, inda take son maimakon haka, take son ya kasance daga cikin Syria ake kai kayan amma ba daga waje ba.
To amma a kusan karshen tattaunawar, sai aka cimma matsaya, Rashar ta jingine wannan ra'ayi nata, ta bari a ci gaba.
A karshen kuriar da mambobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya suka kada kan matsayin, jakadan Amurka a majalisar, ya ce, kwamitin ya yi abin da ya dace, na yanke shawarar da za ta ceci rayuka, da miliyoyin 'yan Syria za su numfasa da jin labarin.