Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dilip Kumar: Waiwaye kan rayuwar tauraron Indiya
Fitaccen dan wasan fina-finan indiya da ya yi tashe a shekarun baya Dilip Kumar, ya rasu a birnin Mumbai, yana da shekaru 98 a duniya.
Kumar ya fito cikin fina-finai sama da 65, a shekaru kusan 50 da ya yi a wannan fannin, inda ya dinga taka muhimman mukamai a duniyar fina-finai ta Bollywood.
A ranar 30 ga watan Yunin 2021 aka kwantar da shi a asibiti, sakamakon matsalar numfashi, duk da cewa yana yawan yin rashin lafiya a watannin da suka gabata.
Ya rasu ya bar matarsa Saira Banu, wadda ita ma jaruma ce a Bollywood. Sai dai ba su taɓa haihuwa ba.
An yi ma sa jana'izar ban girma da yammacin ranar Laraba, kamar yadda ofishin Ministan Maharashtra, Uddhav Thackeray ya sanar tun da fari.
Mr Thackeray ya ce fitattun jaruman fina-finan Bollywood irin su Shah Rukh Khan da Ranbir Kapoor sun kai ziyara gidan mamacin domin yin ta'aziyya.
An yi ta tura sakon ta'aziyyar rasuwar Kumar a shafukan sada zumunta musamman tiwita, ciki har da 'yan siyasa da abokan sana'arsa da masana tarihi.
Wane ne Dilip Kumar
An haifi Dilip Kumar a watan Disambar shekarar 1922 a Peshawar , wanda a yanzu yake Pakistan kafin a raba Indiya.
Kamar sauran 'yan uwansa Musulmai, ya zaɓi sunan mabiya addinin Hindu wato Dilip Kumar, a lokacin da ya shiga masana'antar fina-finan Hindu.
Tauraronsa ya haska a shekarar 1944 a fim din Jwaar Bhata, amma bai daukaka ya zama mashahuri ba sai a shekarar 1949 lokacin da aka saki fim din Andaz.
Cikin fim din soyayyar sun fito tare da jaruma Nargis da Raj Kapoor, wadanda daga bisani suka zama shahararrun 'yan wasa.
Mai rubuta tarihin Kumar, Lord Meghnad Desai ya kwatanta marigayin da dan wasan Hollywood Marlon Brando da na Italiya Marcello Mastroianni.
"An yi ta musun cewa Dilip Kumar shi ne wanda ya fi kowanne daukaka da masana'antar Bolyywood ta taɓa ƙyanƙyashewa.
Akwai taurari wadanda suka fi shi, amma babu wanda ya kai shi daukaka.
Shi ne kyakkyawan dan wasan da ya ke gamuwa da matsaloli a cikin fina-finai, sannan ya shahara a fannin wasan barkwanci,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.
Cikin fina-finan da ya fito da suka yi suna da shahara akwai - Mela da Naya Daur da Ganga Jumna da Devdas da Mughal-e-Azam.
Kumar ya iya fitowa a matsayin attaijiri, talaka, ko baƙauye, da duk wata rawa da aka ba shi domin ya taka.
A shekarun 1970 ne ya fara fitowa a matsayin babban mutum, ko taimaka wa jarumai da sauransu.
"Baya ga fina-finan da yake fitowa a ciki, Dilip Kumar ya taka muhimmiyar rawa a fannin siyasar Indiya, da rayuwar yau da kullum.
Yayin da Indiya ke tasowa bayan samun ƴancin kai, an fuskanci ƙalubale da tsauraran lokuta wanda Kumar na daga cikinsu
An ba shi kyautar ban girma a lokacin bukukuwan kalankuwar fina-finai mafi shahara da aka shirya a kasar.
A shekarar 1966 ne Kumar ya auri Saira Banu, masoyan biyu sun fito a fina-finai da dama kafin su yi aure.
A shekarar 1998 ne Kumar ya fito a fim na karshe.