Bethel Baptist: Shugaban makarantar ya yi waya da ɗalibansu da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

Asalin hoton, Facebook/ The Governor of Kaduna State
Shugaban makarantar sakandiren Bethel Baptist da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya ya ce ya zanta da ɗalibansu da aka sace a ranar Litinin.
Rabaran Ishaya Jangado, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a harabar makarantar, ya ce sun samu damar tattaunawa da 'yan bindigar da suka sace daliban sai dai bai bayyana abin da suka zanta a kai ba.
Ya kara da cewa "mun samu yara 28 da suka kubuta tunda farko" daga cikin jimillar daliban da aka sace a makarantar.
"Na tattauna da biyu daga cikin daliban namu, kuma sun kirga kansu sun gano cewa su 121 ne kuma da muka hada da 28 da aka fara kubutarwa sai muka ga sun cika adadin yawan dalibanmu," in ji Ishaya Jangado.
Tun da farko, kafafen yada labarai a Najeriya sun rawaito cewa dalibai 140 zuwa 150 aka sace.
Amma wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ASP Muhammed Jalige ya fitar ta ce "jami'anmu sun fafari 'yan bindigar ta hanyar amfani da dabaru da makamai kuma sun yi nasarar ceto dalibai 26 ciki har da wata malama guda daya cikin koshin lafiya."
'Yan bindigar sun kai hari a sakandaren Bethel Baptist High School, Damishi da ke Karamar Hukumar Chikun da asubahin Litinin.
Maza da mata
Makarantar ta ƙunshi maza da mata sannan kuma akwai waɗanda ke kwana da kuma masu je-ka-ka-dawo.
"Ɗana da aka ɗauka namiji ne amma wanda ya faɗa mani labarin ya ce 'yarsa aka ɗauka, sai dai sun kuɓuta tare," a cewar Mista Joseph Hayab Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna,
Satar daliban ta sa gwamnatin jihar Kaduna ta rufe makarantun kwana 13 da ke wajen gari tana mai cewa za ta sake bude su ne kawai idan tsaro ya inganta.
Lamarin masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da ta'azzara a Najeriya.
Hakan ne ya sa a watan Yulin bara Majalisar Dattawan kasar ta amince da hukuncin daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a kasar.
A baya dai ana yanke hukuncin daurin shekara 10 ne ga mutanen da aka kama da laifin.











