Abin da ke faruwa a yankin Tigray na kasar Ethiopia da muhimmancinsa

An wallafa

Kasar Ethiopia na ci gaba da mamaye manyan kafafen yada labaran duniya a cikin shekaru kadan da suka gabata, saboda irin bunkasar tattalin arzikin da ta samu cikin sauri da kuma aiwatar da tsarin dimokaradiyya.

Yanzu an wuce lokacin da kasar ta kasance cikin kasashe matalauta a duniya kamar a shekaru da dama da suka gabata.

Amma kuma tana fama da hargitsi na soji da rikicin da ya shafi al'umomi da dama a arewacin yankin Tigray. Halin da ake ciki a kasar zai yi mummunan tasiri a kan makomar kasar da ma makwabtanta.

A halin da aka shiga na baya-bayan nan, dakarun 'yan tawaye sun sake karbe Mekelle babban birnin yankin na Tigray, wanda ya kasance a karkashin ikon gwamnatin kasar tun a cikin watan Nuwamba.

Bari mu duba abubuwan da ke faruwa da kuma yadda aka yi kasar ta samu kanta ciki.

Shin me ke faruwa a Tigray?

A yanzu tashe-tashen hankula a Tigray ba wasu sabbin abubuwa ba ne.

Yanki ne mai jama'ar da suka kai miliyan bakwai, wato a cikin yawan al'umma miliyan 122 na kasar ta Ethiopia.

Mutanen yankin na Tigrayan su ne na uku mafi girma cikin kabilun kasar, baya ga al'ummar Oromo da Amhara.

Akwai matukar nuna kin jinin gwamnatin kasar a wannan yanki, wanda ya sha fama da manyan matsaloli na lokaci mai tsawon da aka shafe ana tafka yakin basasa, wanda ya biyo bayan hambarar da Sarkin Ethiopia na karshe, Haile Selassie, a lokacin wani juyin mulki na shekarar 1974.

Yankin Tigray nan ne tushen matsalar ja'ibar yunwar shekarar 1983 zuwa 1985 da ta haddasa mutuwar mutane miliyan daya kana miliyan biyu suka rasa matsugunansu.

Bayan shafe shekaru da dama na samun kwanciyar hankali, fada ya sake barkewa a cikin watan Nuwambar shekarar 2020 tsakanin dakaru daga gwamnatin yankin na Tigray da kuma na gwamnatin tarayyar kasar.

Me ya sa ake fadan?

Kungiyar masu gwagwarmaya da makamai ta yankin Tigray da ake kira Tigray People's Liberation Front (TPLF) ta kasance daya daga cikin kawancen da ya hambarar da gwamnati a shekarar 1991.

Ta kuma ci gaba da kasancewa kungiya mai karfin fada a ji a siyasar kasar ta Ethiopia har ya zuwa shekarar 2019, lokacin da firaiminista kuma wanda ya lashe babbar kyautar Nobel, Abiy Ahmed, ya kafa sabuwar jam'iyar kawance wacce kungiyar ta TPLF ta ki amincewa ta shiga ciki.

Kungiyar ta ci gaba da kasancewa mai rike da iko a yankin Tigray, kuma a cikin watan Satumbar shekarar da ta gabata ta yi wa gwamnatin Ahmed din tawaye bayan da ta gudanar da na ta zabukan, duk kuwa da dage zabukan kasa baki dayan da gwamnati ta yi a sakamakon annobar korona.

Watanni biyu bayan nan ne, dakarun na TPLF suka kaddamar da hare-hare a kan sansanin sojin Ethiopia. A matsayin mayar da martani, gwamnatin kasar ta kaddamar da na ta hare-haren a yankin na Tigray.

Me muka sani game da wadanda fadan ya shafa?

Gwamnatin tarayya ta kafa dokar hana yada labarai a kan yankin na Tigray, amma kuma an kididdige cewa fadan ya haddasa mutuwar dubban mutane tare da haifar wa da mutane fiye da miliyan biyu rasa matsugunansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da miliyan biyar ne ke bukatar taimakon gaggawa na abinci a yankin, bayan da fadan ya jefa akalla mutane 350,000 cikin fuskantar barazanar ja'ibar yunwa.

An zargi duka bangarorin biyu da keta hakkin bil'adama da kuma kashe-kashen mutane da dama.

Ta yaya yankin Tigray zai shafi zaman lafiyar yankin Gabashin Afirka?

Tashe-tashen hankulan ba kasar Ethiopia kawai ya yi wa mummunan tasiri ba, ya shafi har fadin kasashen da ke makwabtaka da ita.

Dubban 'yan gudun hijira ne suka ketara zuwa kasar Sudan.

Dakaru daga kasar Eritrea makwabciya sun shiga cikin fadan da ake fafatwa a kan dakarun 'yan tawayen na TPLF a cikin watan Nuwamba - duk da cewa yanzu haka halin da ake ciki a yankin na Tigray na ci gaba da kasancewa maras tabbas.

Akwai kuma hadarin cewa mayar da hankalin da gwamnatin tarayya ta yi kan yankin na Tigray ka iya sanyaya yunkurinta na mara wa gwamnatin kasar Somalia baya a kan fadan da ta ke yi da mayakan al-Shabab.

"Yakin ya riga ya zaman a yanki," in ji Rashid Abdi, wani mai sharhi kan al'amuran da suka shafi yankin Gabashin Afirka.

Wasu kwararru kamar Abdi sun jaddada cewa rikicin ka iya sannyaya guiwar kasar ta Ethiopia, da ka iya yin mummunan tasiri kan daukacin yankin.

Misali, zai iya karfafa gwuiwar wasu kungiyoyin da ke kasashe masu yawan kabilu suma su tashi tsaye wajen kalubalantar gwamnatocin su.

Neman sassauta fadan kwana guda bayan barkewar rikicin, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadin cewa "zaman lafiya a kasar Ethiopia na da matukar muhimmanci ga daukacin yankin Gabashin Afirka".

Me kasashen duniya ke cewa?

Kasashen Birtaniya da Amurka da kuma Ireland sun kira zaman tattaunawa kan tsaro na gaggawa a bainar jama'a.

A ranar Litinin ne Sakatare Janar Guterres ya bayyana cewa ya tattauna da Firaminista Ahmed kuma yana "cike da fatan" cewa za a tsagaita wuta.

A halin da ake cikin gwamnatin Ethiopia ta ki amincewa da kiran shiga tsakani na diplomasiyya. A maimakon haka, ta kaddamar da hare-haren da ke da nufin nuna wa kasashen duniya cewa wannan matsalar cikin gida ce.

Gwamnatin ta bayyana rikicin a matsayin "ayyukan jami'an tsaro" a kan "wasu tsiraru" da ke yunkurin tarwatsa dokar tsarin mulkin kasar Ethiopia.