Hotunan Afirka na mako daga 18-24 Yunin 2021: Jajayen fitulu da tayar da ƙura

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga sassan Afirka ko na wasu ƴan nahiyar a sauran sassan duniya a wannan makon, daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Yunin 2021.

Percussionist Malick Fall performing in Saint Louis, Senegal - Friday 18 June 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Juma'a, wani mai kaɗe-kaɗe Malick Fall na bakin aiki a wajen bikin raye-raye na Saint Louis Jazz Festival - bayan da annobar cutar korona ta hana gudanar da bikin a bara.
Angolan singer Anselmo Ralph performing at Super Bock Arena in Porto, Spain - Friday 18 June 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wannan ranar, mawaƙin ƙasar Angolan Anselmo Ralph yana wasa a gaban ɗumbin mutane da ke cikin farin ciki - a birnin Porto na Portugal.
A footballer in front of a red mist in the Olympic Stadium in Rades, Tunisia - Saturday 19 June 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magiya baya sun haskaka filin wasan Olympics na Rades a Tunusia a yayin wasan kusa da na ƙarshe da aka yi tsakanin Esperance da al-Ahly Masar.
Dani Sordo of Spain drives his Hyundai i20 Coupe WRC during the shakedown of the Safari Rally Kenya 2021, Nairobi, Kenya - Wednesday 23 June 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Motocin da ke gasar tsere na tayar da ƙura a Kenya a makon nan a gasar Safari da ake yi, bayan sahfe shekara 19 ba a gudanar da ita ba...
Spectators watch Finnish duo of Kalle Rovanpera and Jonne Halttunen in the shakedown of the Safari Rally in Kenya - Wednesday 23 June 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba, kwana ɗaya gabanin fara gasar, masu gasar sun yi ta atisaye a kan titunan ƙasar.
A boy jumps into the water at Lido beach, Mogadishu, Somalia - Friday 18 June 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Somalia kuwa, wani yaro ya yi tsalle ya faɗa cikin ruwa a ranar Juma'a a babban birnin ƙasar Mogadishu, da takalminsa a ƙafarsa...
Fishermen carry a boat in to the water on Lido Beach, Mogadishu, Somalia - Friday 18 June 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A wannan ranar a bakin teku, wasu masunta sun shirya tsaf don fara su.
Four women taking part in a Saharawi freedom march in Madrid, Spain - Friday 18 June 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne aka kawo ƙarshen jerin macin da aka yi a Sipaniya wanda aka fara a watan Afrilu don kira ga a yi zaɓen raba gardama na son samun ƴancin ƙasar Western Sahara...
A woman at a protest with arm raised women taking part in a Saharawi freedom march in Madrid, Spain - Friday 18 June 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yankin a da yana ƙarƙashin ikon Spaniya ne inda Moroko ta ƙwace shi a 1975 - inda a nan masu zanga-zanga na Saharawi suka yi a Sipaniya suna neman ƙasar ta girmama dokar ƙsa da ƙasa.
Supporters of the opposition collective the Movement for the Defence of Democracy at a rally in Dakar, Senegal - Wednesday 23 June 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma wasu masu zanga-zangar goyon bayan ƴan hamayya a Senegal ne ke nuna adawa da tazarce ɗin shugaban ƙasar a karo na uku a ranar Laraba.
Women with arms raised practising yoga in Johannesburg, South Africa - Saturday 19 June 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu motsa jiki na Yoga suna ta famar motsa jiki a ranar Asabar don girmama ranar Yoga, a birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu.
A refugee stands in Goudebou camp in northern Burkina Faso - Sunday 20 June 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi bikin Ranar Ƴan Gudun Hujira Ta Duniya - a wannan hoton kuma wani ɗan Mali ne da ya tsereyake tsaye a sabon matsuguninsa da ke Goudebou, wani sansani da ke da mutum 11,000 a arewacin Burkina Faso.
Voters queue up at a polling station for the parliamentary and regional elections in Beshasha, Ethiopia - Monday 21 June 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin a Habasha, masu zaɓe sun yi layi a wata maza a Beshasha, ƙauyen da Firaminista Abiy Ahmed ya fito.
A woman prepares fufu, made from pounded cassava, in Monrovia, Liberia - Saturday 19 June 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata mata na dafa Fufu, wanda ake yi da rogo a Monrovia, babban birnin Laberiya a ranar Asabar. Ana yawan cin fufu da miyar geebee wacce aka yawan yi a gundumar Nimba.
A man pulls a cart laden with reed chairs in an impoverished settlement of Hopley, Harare, Zimbabwe - Wednesday 23 June 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum a Zimbabwe ya ɗebo kwandunan kaba a cikin amalanke a ranar Laraba a Hopley, wani yanki a birnin Harare na Zimbabwe.

Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka.