Bincike ya gano labarin matar da ta haifi ƴan 10 a Afirka Ta Kudu ba gaskiya ba ne

Asalin hoton, African News Agency (ANA)
Wani bincike da hukumomi suka gudanar ya gano cewa labarin da aka bayar a farkon watan nan da ke cewa wata mata 'yar kasar Afirka Ta Kudu mai suna Gosiame Sithole ta haifi 'yan 10 ba gaskiya ba ne.
Gwamnatin lardin Gauteng ta ce babu wata shaida a hukumance da ta nuna cewa matar ta haifi 'yan 10.
Wasu gwaje-gwajen kimiyya da aka gudanar sun nuna cewa Ms Sithole ba ta dauki ciki ba a baya bayan nan, in ji wadanda suka gudanar da binciken.
Yanzu haka matar mai shekara 37 tana karkashin kulawar jami'an lafiya inda ake duba lafiyar kwakwalwarta.
Sanarwar da aka fitar kan batun ba ta yi karin bayani kan dalilin kitsa labarin na karya ba.
Kamfanin Independent Online (IOL), wanda ya mallaki jaridar Pretoria News da kuma shi ne na farko da ya wallafa labarin, ya dage cewa labarin gaskiya ne.
Ya yi ikirarin cewa Ms Sithole ta haifi 'ya'yan ranar 7 ga watan Yuni a asibitin Steve Biko Academic Hospital (SBAH) da ke babban birnin kasar, Pretoria, yana mai cewa ma'aikatan asibitin ba su shirya karbar haihuwar ba.
Ya zargi asibitin da kuma gwamnatin lardin da yunkurin yin rufa-rufa kan sakacin aiki.
"Wadannan zarge-zarge karya ce da ba ta da tushe wadda ke da zummar bata sunan asibitin Steve Biko Academic Hospital da kuma Gwamnatin Lardin Gauteng," a cewar sanarwar da aka fitar kan batun.
Sanarwar ta kara da cewa za a dauki mataki na shari'a kan babban editan jaridar Pretoria News, Piet Rampedi, da kuma kamfanin IOL.
Daga ina aka samu labarin?
Ms Sithole, wadda ke da 'yan tagwaye masu shekaru shida, da abokin zamanta Teboho Tsotetsi suna zaune a garin Thembisa, da ke lardin Gauteng kusa da birnin Johannesburg.
A cewar IOL, suna halartar coci guda da Rampedi inda aka gabatar masa da su a watan Disamba. A watan Mayu an yi zargin cewa ya yi hira da ma'auratan wadanda suka ce suna sa ran za su haifi 'ya'ya takwas - wani hoto ya nuna Ms Sithole dauke da juna biyu niki-niki.
Ranar 8 ga watan Yuni ne jaridar Pretoria News ta bayar da labarin abin mamaki na haihuwar 'ya'ya goma inda ta ambato Mr Tsotetsi a matsayin mutumin da ya ba ta labarin. Daga bisani ya ce ya samu sakonni a rubuce na waya daga abokiyar zaman tasa inda ta gaya masa ta haihu, yana mai karawa da cewa an hana shi zuwa asibitin saboda cutar korona.
Kazalika Rampedi ya dogara ga sakonni WhatsApp - kuma bai samu wata majiya mai zaman kanta daga asibitin ba game da sahihancin labarin.
Daga nan ne magajin garin ya tabbatar da haihuwar - wanda a wancan lokacin ne kafafen watsa labarai, ciki har da BBC, suka wallafa labarin - amma daga bisani wani kakakin gwamnati ya ce dan siyasar ya ji labarin ne kawai daga wurin iyalin da lamarin ya shafa kuma babu wanda ya ga jariran da aka haifa.
An rika aike wa da gudunmawa ga ma'auratan da kuma jariran da aka bayar da labarin sun haifa, wadanda aka yi wa lakabi "Thembisa 10", ciki har da kyautar rand miliyan daya ($70,000; £50,000) daga shugaban IOL Iqbal Survé.
Sai dai an soma nuna shakku kan labarin bayan jaridar Pretoria News ta gaza sanar da asibitin da aka haifi jariran kuma asibitoci da dama a lardin na Gauteng sun fito sun karyata hannunsu a labarin.













