Covid-19: Za a tsawaita dokar kulle a faɗin Ingila da mako huɗu

An wallafa

Manyan ministocin gwamnatin Birtaniya sun amince da a jinkirta dage matakan kullen da aka sanya wa Ingila har zuwa bayan ranar 21 ga watan Yuni.

Wata majiya mai ƙarfi ta sanar da BBC cewa yawancin dokokin kullen za su ci gaba da aiki na tsawon makonni huɗu bayan wannan ranar.

Wannan na nufin za ci gaba da kulle gidajen shakatawa kuma za a bukaci mutane su ci gaba da aiki daga gida.

Firaminista Boris Johnson zai tabbatar da sabon matakin a cikin yinin yau yayin wata ganawa da zai yi da manema labarai.

Sai dai wannan jinkirin zai iya janyo wasu 'yan jam'iyyarsa ta Conservative su yi wa gwamnatin bore, domin za a kada kuri'a kan batun a karshen wannan watan a majalisar kasar wato House of Commons.

Ana samun karuwar masu kamuwa da wani nau'i na kwayar cutar korona mai suna 'Delta', wanda aka fara gani a India, wanda kuma ya kama kashi 90 cikin 100 na dukkan masu kamuwa da cutar a ƙasar.

A ranar Lahadi, Birtaniya ta sanar da cewa mutum 7,490 sun kamu da Covid-19, kuma mutum takwas sun mutu.