Likita: 'Bayar da tallafin jini na kara lafiya'

An wallafa

Yau ce ranar ba da gudunmawar jini ta duniya, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kebe a duk shekara.

Hukumar ta ware ranar don wayar da kan al'umma kan buƙatar samar da jini da kuma nusar da gwamnatoci muhimmancin adana jinin.

Likitoci dai na shawartar jama'a da su riƙa ba da jini domin samun lafiya baya ga ceton rayuwar al'umma.

Dakta Zubairu Jimoh darekta a cibiyar tattara jini ta Najeriya da ke Abuja, ya shaidawa abokin aikinmu Usman Minjibir cewa ba kai tsaye ake fara dibar jinin ba, ana bin wasu matakai kama daga tantance ko mutum ya na da isasshen jinin bayarwa da sauransu.

'Dalilin da ya sad an adam zai bada jinni abu ne da ya dace, mutane bisa radin kan su, ba sai an matsa musu ba ko biyansu wasu kudade su bada tallafin jinin.

Da farko sai ma mun duba mu ga shin nawa ne yawan jinin da ke jinkinsu, abin da muke kira a turance da HB, mu tabbatar da lafiyarsa, sannan idan jinin ya wadata a jikinsa za mu dauki Mil 45 kadai muke diba, saboda baki daya jinin da ke jikin dana dam Lita 7 ne da doriya,'' inji Dakta Zubairu.

Dakta Zubairu ya kara da cewa amfanin bada jini ya na da yawa ga lafiyar dan Adam. Abu na farko shi ne karawa mutum karfin jiki, da kuzari, sannan idan namiji zai iya badawa zai iya bada tallafin jini sau 3 zuwa 4 a kowacce shekara.

''Hatta mata su na iya bada jinin, sai dai bai fi su 2 ko 3 ba sakamakon jinin al'ada da suke yi kowanne wata. Wannan jini da ake ajiyewa a sibiti ya na da matukar amfani, misali akan kawo mace mai juna biyu da ta zo haihuw aka samu tangarda ta zubda jini, ka ga Kenan wannan ana bukatar kara ma ta jini don haka wanda aka ajiye zai yi amfani Kenan. Sannan akawai masu lalurar Amosanin jini wato Sickle Cell a turance, su ma sun a bukatar Karin jini.''

Ta kowace fuska bada tallafin jini da ajiye shin a da matukar muhimmanci kuma aiki guda suke yi, wato ceton ran marasa lafiyar da ke tsananin bukatar kara ma sa jini.