Amurka na bincike kan wasu abubuwa da ke yawo a sararin samaniyarta

An wallafa

Wani rahoton gwamnatin Amurka kan ganin wasu abubuwa masu tashi sama da ba a san ko meye ba (UFOs), ya gano cewa babu wata shaidar cewa akwai wasu halittu na 'alien' amma ba su cire tsammanin akwai ba.

Ana sa rai bitar da aka yi kan ganin abubuwan masu tashi sau 120 zai yanke cewa babu sa hannun fasahar Amurka a mafi yawan lokutan da abin ya faru.

Baya ga haka, rahoton bai yi wani cikakken bayani kan ko mene ne abubuwa da ke tashi saman ba, a cewar jami'ai.

Za amiƙa wa ƴan majalisar dokoki rahoton da ba na sirri ba a watan Yuni.

Rahoton dai sakamakon wani kwamitin soji ce da aka kafa a bara don bincike kan abubuwan da ake gani a sararin samaniyar Amurka tsawon shekaru.

Ma'aikatar tsaro ta ce tana so ta "ƙara fahimtar" lamarin ko abubuwan (UFOs) da ake gani kuma ta duba idan za su iya zama barazana ga tsaron ƙasar.

Fitar da rahoton ya ja hankalin jama'a a Amurka inda aka daɗe ana tattaunawa kan ganin abubuwan masu tashi da jita-jitar cewa akwai wasu halittu da ke rayuwa a wata duniyar.

Masu sha'awar batun UFO na ta ce-ce-ku-ce kan abin da rahoton ya ƙunsa kafin miƙa shi ga majalisar ranar 25 ga watan Yuni.

Me muka sani game da rahoton?

Bayanan da ke ƙunshe cikin rahoton sun fara bayyana ne a rahoton jaridar New York Times da CNN da Washington Post ranar Alhamis.

Kafofin yaɗa labaran sun ce sun yi magana da jami'an gwamnati da dama kan abin da aka gano a rahoton da aka ƙagu a fitar.

Jami'an sun ce cikin ganin abubuwan da ke tashi sama da aka yi sau 120 a shekaru ashirin ɗin da suka gabata, mafi yawa jami'an sojin ruwan Amurka ne suka yi yayin da wasu kuma dakarun ƙasashen waje ne suka yi.

CNN ta ce ta yi magana da wasu majiyoyi guda uku waɗanda suka ce rahoton bai cire tsammanin akwai wasu halittu da ke rayuwa a wajen duniyar mu ba.

Sai dai babu shaidar cewa abubuwan da ake gani suna yawo a sararin samaniya da matuƙa jirgin rundunar soji suka gani a shekarun baya-bayan nan, jirgin halittun e, jaridar New York Times ta ruwaito.

Jaridar ta ce jami'an leƙen asiri sun ce akwai yiwuwar cewa ƙasashe masu ƙarfin iko da ke adawa da Amurka kamar China ko Rasha ne ke gwajin sabbin fasahohinsu a sararin samaniyar.

Jaridar da CNN sun ce jami'an leƙen asiri sun damu game da tasirin da wannan hasashe zai yi ga tsaron ƙasar.

Waɗanne halittu aka taɓa gani aka kai rahoto?

An yi magaa kan ganin wasu halittu a wani sabon rahotin CBS News kuma wannan ya sake ɗaukar hankula kan batun a watan da ya gabata.

Shirin kafar yaɗa labaran na 60 Minutes ya tattauna da wani matuƙin jirgin sama na rundunar sojin ruwan Amurka wanda ya ce sun ga wani jirgi da ba su taɓa ganin irinsa ba ya wuce su da saurin gaske kuma yana kukkurɗawa ba kamar yadda aka saba gani ba.

Wani matuƙin jirgi da a yanzu ya yi ritaya, Ryan Graves ya ce bataliyarsa ta matuƙa jirgin yaƙi sun fara ganin wasu abubuwa suna yawo a sararin samaniya a filin da aka taƙaita tashi kusa da Virginia a shekarar 2014.

Ya ce abun ko jirgin ba shi da salansa inda hayaƙi ke fita kuma yana tafiya ne da saurin da ya wuce yadda fasahar da ake da ita yanzu ta sani.

Mista Graves ya ce matuƙa jirgi da ke atisaye a gaɓar tekun Atlantic sun sha ganin irin wannan abun "kusan kullum tsawon shekaru a ƙalla biyu".

A cikin watan da ya gabata, Luis Elizondo, wani tsohon jami'in leƙen asiri na Amurka ya shaida wa ABC NEWS cewa wasu daga cikin abubuwan ko jiragen da aka gani a saman suna tashi "na iya zarce duk wani abu da muke da shi na fasaharmu."

"Abin tambayar shi ne, mene ne wannan?" ya ce. "Gaskiyar magana ita ce, ba mu sani ba."

A watan Afrilun bara, Ma'aikatar Tsaron Amurka ta fitar da wasu bidiyo na abin da ta ce ya nuna "wani abu a sama da ba a yi bayani a kan shi ba".

Ma'aikatar ta ce tana so ta "goge duk wasu jita-jita da mutane ke yi kan bidiyon", wanda aka taɓa sakinsa ba bisa ƙa'ida ba a 2007 da 2017, "idan gaskiya ne".