Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
United Africa Republic - Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan sauya wa kasar suna zuwa UAR
A yayin da ake zaman jin ra'ayoyin 'yan Najeriya kan sauya kundin tsarin mulkin 1999, ana ta yada rahotannin cewa an gabatar wa majalisar wakilai bukatar a sauya sunan kasar zuwa "United Africa Republic".
Rahotanni sun ce daga cikin 'yan Najeriyar masu bayyana ra'ayoyinsu a zauren majalisar ne wani ya gabatar da wannan bukata.
Ita ma fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga wannan lamari, inda ta ce ba ita ta gabatar da ƙudurin sauya sunan ƙasar ba.
Mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa a shafin Tuwita cewa Shugaba Buhari ba shi da hannu a batun sauya sunan.
"Ba gwamnatin Najeriya ko SHugaba Buhari ne suka miƙa buƙatar sauya sunan ba, mutane ne ƴan ƙasa suka yi hakan a wajen jin ra'ayoyin jama'a.
"Amma tuni wasu mutane suka ɗauki abin suka ɗora a ka suna zargin shugaban ƙsa wanda ba shi da hannu sam a ciki," a cewar saƙon na Bashir.
Sai dai wannan kudurin na bukatar amincewa kafin a kai ga tabbatar da sabon sunan. Akwai kasashen Afirka da dama da suka sauya sunayensu a bisa wasu dalilai.
Wannan labari shi ne ya fi jan hankalin 'yan kasar a ranar Alhamis musamman matasa a shafukan sada zumunta da muhawara.
Maudu'in United African Republic da aka kaddamar a Tuwita shi ne na biyar mafi tashe inda aka yi amfani da shi fiye da sau 70,000 zuwa karfe uku na yammacin ranar.
Mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyi daban-daban inda wasu suka mayar da abin raha, wasu kuma suka nuna hakan ci gaba ne mai kyau.
Sai dai wasu na ganin hakan ba abu ne mai muhimmanci ba don ba sauya suna ne matsalar Najeriya ba a yanzu.
Wasu har sun fara sanya hotunan kudi na raha da sabon sunan na United Africa Republic.
Wasu labaran da za ku so
Me mutane ke cewa?
@kvng_rhamzy ta ce: "Saboda kasashe irin su United States (Amurka) da United Kingdom (Birtaniya) da United Arab Emirates (Hadaddiyar Daular Larabawa) sun ci gaba ne shi ya sa wasu ke son a sauya wa Najeriya suna zuwa UNITED AFRICAN REPUBLIC?
@Symply_Tacha cewa ta yi: United African Republic?? Ba sauya wa Najeriya suna ne matsalar 'yan Najeriya ba!!! A ba mu tituna masu kyau, a samar da tsaro da wutar lanytarki da ingantaccen tsarin lafiya... Kawai a samar mana abubuwan more rayuwa.
Ada-Eze ta ce: "Matsalar Najeriya fa ba a suna ba ne a ainihin yadda aka kafa kasar ne. Sauya sunan Najeriya zuwa United African Republic tamkar sauya sunan kamfanin wutar lantarki na NEPA ne zuwa PHCN, amma har yanzu babu wutar. Lokaci ya yi da za mu daina mafarki mu fuskanci ainihin abin da ke faruwa.
Frank Donga cikin raha ya ce: "Ku tsaya, idan aka sauya sunan zuwa United African Republic, me zai faru da dafadukar shinkafa ta Najeriya?
A shafinmu na Facebook ma mutane sun yi ta yin tsokaci kan wannan batu har sau sama da 3,000, ga kuma abin da wasu ke cewa: