Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kashmir: Mahaifin da ya shiga tonon gano gawar ɗansa da ya ɓata
A watan Agustan bara ne wasu mutane su ka yi garkuwa da wani soja a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya.
Iyalin shi sun yanke ƙauna cewa yana raye.
To amma a yanzu mahaifinsa ya ce ba zai numfasa ba har sai ya gano gawar ɗansa.
Kwana ɗaya bayan Manzoor Ahmad Wagay ya samu labarin sace ɗansa, ƴan sanda sun gano motarsa a wani wuri.
Kilomita 15 daga wurin kuma sai ga ƙarnin jini da kuma rigar da ya je sanye makale a kan wata bishiya an yayyaga ta.
Daga nan sai jikin masu binciken ya yi sanyi.
Da yammacin ranar 2 ga watan Agustan 2020 ne Shakir Manzoor mai shekaru 24 ya gudanar da bikin Sallah a gidansu tare d danginsa da ke Shopian gundumar Himalayan.
Kamar yadda iyalinsa suka bayyana, Shakir wanda musulmi ne daga Kashmir na aiki ne da rundunar sojin Indiya, kuma yana kan hanya zuwa sansaninsa da ke da nisan kilomita 17 ne a lokacin da yan aware suka tsayar da motarsa.
''Wasu daga cikin su ne suka shiga motar suka tuka da shi a ciki kuma tun lokacin ba mu sake jin ɗuriyarsa ba'', a cewar kanin shi Shahnawaz Manzoor, wanda ya ce sun samu wannan bayani ne ga wadanda suka gane wa idonsu abin da ya faru.
Fiye da watanni tara da sace Shakir, har yanzu Manzoor na ci gaba da neman gawar ɗansa.
Ya fara bincikensa ne daga ƙauyen da aka tsinci rigar ɗan nasa, zuwa abin da ya kewaye fadin kilomita 50 a dajin, wanda ke da itatuwa da ƙoramu da kuma wasu ƙauyukan zagaye da shi.
Shahnawaz ya bar makaranta bara don taimaka wa mahaifinsa. Sun kuma dauki hayar diga don tonon ramuka da ke yankin Himalaya.
''Abokanmu da ma makwabtanmu sukan zo da kayan gini don taimaka mana a duk lokacin da muke aikin nemo gawar.'' a cewar Shahnawaz.
Wata rana suna cikin aikin suka gino gawar wani dajjito a yankin da ake zargin yan aware sun sace tare da kashe shi.
Ba a jima ba da sifetan 'yan sandan yankin Dilbag Singh ya sanar da cewa neman inda Shakir yake bai ƙare ba, duk da bai bayyana halin da ake ciki game da binciken ba.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin hukumar yan sandan yankin amma ba su amsa gayyatar tattauwana da su kan batun ba.
Kamar yadda dokar yankin ta shata ana bayyana mutun a matsayin matacce matsawar aka yi shekaru bakwai ana neman shi ba a gans shi ba, saboda haka za a iya cewa Shakir ya bata.
''Ɗana ya sadaukar da rayuwarsa ga ƙasar nan. Idan ya shiga ƙungiyar ƴan tawaye ne su fito fili su faɗa. Idan ma ƴan tawaye sun kashe shi me ya sa za a rika boye mana?'' in ji Shahnawaz.
Lura da yadda rikici yaƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin Kashmir, ba abun mamaki ba ne mutane su riƙa ɓata ba tare da an gano su ba.
Amma gari irin Shopian da ke zagaye da sojoji ta ko'ina, kuma yake kilomita 80 tsakanin shi daga birnin Srinagar, batan soja na da mamaki.
Mr Wagay wanda manomi ne mai ƙaramin karfi ya bayyana cewa akwai jami'an tsaro da dama da iyalansu ke rasa su a bakin daga tsawon lokaci.
Ya ce a baya ya gargaɗi ɗansa da kada ya shiga aikin soji amma bai ji ba.
''Ya ƙi jin magana ta saboda yana da sha'awar shiga aikin soji. Matsalar ita ce ba zai iya bambancewa tsakanin Musulmi da mabiya Hindu ba.'' In ji Wagay.
A yanzu sun mayar da hankali wurin neman addu'o'i daga malaman addini wataƙila a dace.
Duk da haka ya ce ''na fara gajiya da zuwa wurin malamai,'' kamar yadda ya faɗa wa matarsa.
Mr Wagay ya yanke shawarar komawa daji wurin ci gaba da neman ɗansa.
''Allah Ya ba mu komai. Mun san cewa ya mutu tun ranar da muka tsinci kayansa. Tuni mun yi masa sallar jana'iza''.
''To amma matsawar ina raye zan ci gaba da neman inda gawarsa ta ke,'' inji Wagay.