Hotunan yadda aka yi zanga-zangar adawa da Isra'ila a kasashen duniya

An wallafa

Mutane a kasashen duniya daban-daban ne suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hare-haren Isra'ila a Gaza da kuma batun mamaye yankunan Falasdinawa.

An gudanar da zanga-zangar a ƙasashen Turai da Amurka da Ajantina da Indonesiya da Iran.

Ma'aikatar Lafiya da ke karkashin ikon Hamas ta ce, zuwa yanzu fiye da mutum 200 ne suka mutu, da suka hada da yara 59 da mata 35, sannan a kalla mutum 1,305 ne suka jikkata.

palestine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata yarinya na rike da allo mai launin tutar Falasdinu yayin wata zanga-zangar adawa da mamayar da Isra'ila ke yi wa Falasdinu. Masu zanga-zangar sun taru ne a Dandalin Courthouse a Dayton, da ke birnin Ohio na Amurka.
palestine

Asalin hoton, SOPA Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar suna fatan Isra'ila ta sakar wa Falasdinawa mara.
palestine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama ne suka fito tattakin na Ohio
palestine

Asalin hoton, Getty Images

Demonstrators take part in a protest against Israel, in Jakarta on May 18, 2021, amid the ongoing conflict between Israel and the Palestinian Territories. (Photo by BAY ISMOYO / AFP) (Photo by BAY ISMOYO/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Jakarta na Indonesia ma an yi irin wannan zanga-zangar a ranar Talata 18 ga watan Mayu.
Several associations demonstrated in Rieti, Italy, on May 17, 2021 calling for an 'immediate ceasefire' in Palestine. Arab families living in the city and political representatives were present, with the participation of Arci, Partito Democratico, PSI, CGL and UIL, Sinistra Italiana, Rifondazione Comunista, Partito Comunista and ArciGay. (Photo by Riccardo Fabi/NurPhoto via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Italiya ma an yi irin wannan zanga-zangar ranar Litinin 17 ga watan Mayun, inda suke kira da a tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Faladinu. Larabawa mazauna kasar da wakilan siyasa na daga cikin wadanda suka halarci zanga-zangar.
BUENOS AIRES, ARGENTINA - MAY 17: People gather to stage a demonstration in support of Palestinians and to protest against Israeli attacks on Gaza Strip in front of Israel's Buenos Aires Embassy in Buenos Aires, Argentina on May 17, 2021. (Photo by Muhammed Emin Canik/Anadolu Agency via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Buenos Aires na Ajantina ma dandazon mutane ne suka taru don yin irin wannan zanga-zanga a ranar Litinin 17 ga watan Mayu.
Fully-veiled Iranian protesters wave Palestinian national flags during a protest to condemn the ongoing Israeli air campaign on Gaza at Palestine Square in central Tehran, on May 18, 2021. - The UN Security Council was to hold an emergency meeting amid a diplomatic push to end the devastating conflict between Israel and Gaza's armed groups that has killed more than 220 people, most of them Palestinians. (Photo by ATTA KENARE / AFP) (Photo by ATTA KENARE/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matan Iran sanye cikin hijabai da nikabi sun ma sun yi irin wannan zanga-zangar a birnin Tehran, ranar Talata 18 ga watan Mayu

Dukkan hotuna na da hakkin mallaka