Chelsea vs Manchester City: A Portugal za a yi wasan karshe na Champions League

An wallafa

Za a gudanar da wasan karshe na Champions League tsakanin Chelsea da Manchester City a Portugal inda 'yan kallo 6,000 daga kowacce kungiya za su halarce shi.

Wasan da za a fafata ranar 29 ga watan Mayu, an mayar da shi birnin Porto na kasar Portugal daga kasar Turkiyya sakamakon kullen korona.

Filin wasan Porto yana iya daukar mutum 50,033

Portugal na cikin kasashen da Ingila ta kyale 'yan kasarta su je don haka 'yan kwallo da magoya bayansu za su iya zuwa ba tare da an killace su idan suka koma gida.

Turkiyya na cikin kasashen da Birtaniya ta dakatar da 'yan kasarta daga zuwa.

Wannan ce shekara ta biyu da za a yi wasan karshe na gasar ta Champions League a Portugal.

"Ba za mu hana magoya baya zuwa kallo kafa-da-kafa ba kuma ina farin ciki da aka samu matsaya," in ji shugaban Uefa Aleksander Ceferin.

Uefa da jami'an gwamnatin Birtaniya da kua na hukumar kwallon birtaniya sun tattauna kan yiwuwar yin wasan a filin wasa na Wembley sai dai an gaza cimma matsaya kan batun killlace manyan mutane, da masu daukar nauyin gasar da 'yan jarida.