Bob Marley: Shekara 40 bayan rasuwar shahararren mawakin rege

An wallafa

Yau shekara 40 ke nan tun bayan rasuwar fitaccen mawakin nan na rege Bob Marley sakamakon cutar daji wato kansa a Miami, yana da shekara 36.

Ya mutu ne ranar 11 ga watan Mayu na 1981. Mun zabo muku wasu hotuna na rayuwarsa:

Bob Marley lokacin da ya je birnin London a 1977

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley lokacin da ya je birnin London a 1977

Mawakin yana daya daga cikin mawakan da suka fi shahara kuma ake matukar kaunarsa a fagen waka a tarihi, inda ya rera fitattun wakokin da suka hada da No Woman No Cry, One Love, da kuma Redemption Song.

Bob Marley ya yi waka a kasar Netherlands a 1977

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley ya yi waka a Houtrust Hallen da ke birnin Hague na kasar Netherlands, a 1977 (hoton sama da na kasa)
Bob Marley performs on stage in the Netherlands

Asalin hoton, Getty Images

Wakar Buffalo Soldier ita ce wakarsa da ta fi shahara a Birtaniya, inda ta zama ta hudu a watan Mayun 1983.

Mujallar Time ta ayyana kundin wakar da ya fitar a 1977 mai suna Exodus a matsayin Kundin Karni.

Bob Marley yana waka a Amurka a 1979

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley yana waka a Amurka a 1979

An haifi Marley a shekarar 1945 kuma mahaifinsa farar fata ne yayin da mahaifiyarsa bakar fata ce 'yar kasar Jamaica.

Ya shafe rayuwar yarintarsa a cikin talauci kuma bai faye ganin mahaifinsa ba, wanda sojan ruwa ne da ya yi aiki da gwamnatin Birtaniya.

Ya bar gidansu yana da shekaru 14 domin yin sana'ar waka a Kingston.

A shekarar 1972, Marley ya isa Birtaniya tare da tawagarsa mai suna The Wailers inda suka rika zaga kasar tare da Johnny Nash yana fatan kaddamar da sana'ar wakarsa ga duniya.

Bob Marley da The Wailers a London

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mawakan The Wailers (Earl Lindo, Aston Barrett, Bob Marley, Peter Tosh, Carlton Barrett da Bunny Wailer) sun dauki wannan hoton a 1973 a London

Shekara guda bayan haka, The Wailers suka fitar da kundin wakoki mai suna Catch a Fire sannan suka fito a hirar talbijin a BBC.

Hirar da suka yi ta yi gagarumin tasiri inda suka samu masoya a kasashe daban-daban.

Bob Marley da the I-Threes (Judy Mowatt, Rita Marley and Marcia Griffiths) suna waka a Dandalin the Rainbow a London a 1977

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley da the I-Threes (Judy Mowatt, Rita Marley and Marcia Griffiths) suna waka a Dandalin the Rainbow a London a 1977
Bob Marley yana waka a wani otal a London a 1978

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley yana waka a wani otal a London a 1978

A wani balaguron waka da ya yi a 1975, sun rera wakar No Woman No Cry kai-tsaye a The Lyceum, London, inda aka saki wakar lamarin da ya bai wa Marley shahararsa ta farko a Birtaniya.

Daga nan mawakin ya shiga waka gadan-gadan inda aka san shi a ko ina a fadin duniya.

Bob Marley ya yi waka a West Coast Rock Show da ke Ninian Park a birnin Cardiff, a 1976 (hoton sama da na kasa)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley ya yi waka a West Coast Rock Show da ke Ninian Park a birnin Cardiff, a 1976 (hoton sama da na kasa)
Bob Marley performs at the West Coast Rock Show at Ninian Park in Cardiff, Wales, in 1976

Asalin hoton, Getty Images

An san Marley a matsayin mai bin addinin Rastafaria, shi da matarsa Rita, inda suke sanya addinin nasu a cikin wakokinsa.

Bob Marley szaune a teburi yana rike da biro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley a Hollywood Tower Records, California, Amurka a shekarar 1979

Mawakin yana matukar son kwallon kafa kuma yakan murza leda kafin ya rera waka ko kuma bayan ya gama.

Bob Marley on a football field in Rio de Janeiro, Brazil, in 1980 with football player Paolo Cesar Caju and singer-songwriter Chico Buarque

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Bob Marley (tsakiya) tare da dan kwallo Paolo Cesar Caju (hagu) da marubucin wakoki Chico Buarque (dama) a filin kwallo a birnin Rio de Janeiro, Brazil, a 1980

"Ina son waka da kwallon kafa," a cewarsa a wata hira da ya yi a 1980.

Marley ya rera wakarsa ta karshe kai-tsaye a Birtaniya ranar 13 ga watan Yulin 1980 a New Bingley Hall, Stafford.

Marley ya mutu shekara daya bayan haka sakamakon cutar kansa, wadda aka gano yana dauke da ita a 1977. An binne shi a kauyensu Nine Mile da ke kasar Jamaica.

Bob Marley seen in 1978

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bob Marley ya dauki wannan hoton a 1978

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.