Kayatattun hotunan Afirka na mako: Daga 30 ga watan Afrilu zuwa 6 ga watan Mayu na 2021

An wallafa

Mun zabo muku fitattun hotunan Afirka na wannan makon:

Wata yarinya ke nan ranar Laraba tana tunani kan wasan dara ko chess a Turancin Ingilishi da ke Makoko, wani wuri a Legas da ke Najeriya...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata yarinya ke nan ranar Laraba tana tunani kan wasan dara ko chess a Turancin Ingilishi da ke Makoko, wani wuri a Legas da ke Najeriya...
Wata mata a birnin Legas take sayar da goro ga mutanen da suka halarci tattakin da aka yi don bikin ranar ma'aikata ranar Asabar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata mata a birnin Legas take sayar da goro ga mutanen da suka halarci tattakin da aka yi don bikin ranar ma'aikata ranar Asabar.
Wasu yan mata biyu suna duba wayar hannu ranar Juma'a a wani taron bikin addini na Good Friday da aka yi a Addis Ababa, babban birnin Habasha...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu yan mata biyu suna duba wayar salula ranar Juma'a a wani taron bikin addini na Good Friday da aka yi a Addis Ababa, babban birnin Habasha...
A birnin Addis Ababa, an ga tururuwar kiristoci zuwa kasuwa ranar Asabar suna siyan kaji domin dafa abincin bukukuwan Easter

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Addis Ababa, an ga tururuwar kiristoci zuwa kasuwa ranar Asabar suna sayan kaji domin dafa abincin bukukuwan Easter
Tsoffin sojoji a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia suna murnar zagayowar ranar tunawa da kawo karshen mamayar Italiya a 1941.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tsoffin sojoji a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia suna murnar zagayowar ranar tunawa da kawo karshen mamayar Italiya a 1941.
Nan kuma wata Bayahudiya ce ta kunna kyandir a wurin ibada ta Ghriba a tsibirin Djerba da ke Tunisia ranar Juma'a...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma wata Bayahudiya ce ta kunna kyandir a wurin ibada ta Ghriba a tsibirin Djerba da ke Tunisia ranar Juma'a...
A bikin, ana rubuta addu'oi kan kwayaye, wata al'ada da aka dade ana yi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A bikin, ana rubuta addu'oi kan kwayaye, wata al'ada da aka dade ana yi.
Wata malamar jinya riƙe da ruwan allurar rigakafin Pfizer da BioNTech a wata cibiyar yin allurar a Tunis, babban birnin Tunisia ranar Litinin.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata malamar jinya riƙe da ruwan allurar riga-kafin Pfizer da BioNTech a wata cibiyar yin allurar a Tunis, babban birnin Tunisia ranar Litinin.
Wani dan Libya ke nan ranar Juma'a yana hawa kan tsauni inda yake fadawa ruwa domin iyo a Tripoli, babban birnin kasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani dan Libya ke nan ranar Juma'a ya yi daka-tsari domin fadawa ruwa daga kan dutse a Tripoli, babban birnin kasar.
A dai ranar, wasu tsuntsaye suna bi ta saman wata gada da ke saman Kogin Nijar a Bamako da ke Mali.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai ranar, wasu tsuntsaye suna bi ta saman wata gada da ke saman Kogin Nijar a Bamako da ke Mali.
Sabon zakaran kambin ajin masu nauyi Francis Ngannou da ake kira "The Predator", na rangadi a birnin Bafoussan ranar Lahadi bisa nasarar da ya samu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sabon zakaran kambin ajin masu nauyi Francis Ngannou da ake kira "The Predator", na rangadi a birnin Bafoussan ranar Lahadi bisa nasarar da ya samu.
Yadda wata mata take juye madarar da suka tatsa daga rakuma a roba ranar Talata a N'Djamena da ke Chadi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda wata mata take juye madarar da suka tatsa daga rakuma a roba ranar Talata a N'Djamena da ke Chadi.
Wani mai sassaka gumaka dan Zimbabwe, Zimbabwea yana nuna daya daga cikin ayyukansa da ke nuna sassakar mace sanye da takunkumi a birnin Harare ranar Juma'a.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai sassaka gumaka dan Zimbabwe, Zimbabwea yana nuna daya daga cikin ayyukansa da ke nuna sassakar mace sanye da takunkumi a birnin Harare ranar Juma'a.
Nan kuma shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ce ke shirin yi wa majalisar dokokin Kenya jawabi ranar Laraba sanye da takunkumi - wani abu da bata cika yi ba a kasarta.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Nan kuma shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ce ke shirin yi wa majalisar dokokin Kenya jawabi ranar Laraba sanye da takunkumi - wani abu da bata cika yi ba a kasarta.
A ranar Larabar, an gudanar da bukukuwa lokacin ziyarar tata duk da cewa ruwan sama ya ritsa da yan sandan Kenya da ke jiran yin kade-kade.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Larabar, an gudanar da bukukuwa lokacin ziyarar tata duk da cewa ruwan sama ya ritsa da yan sandan Kenya da ke jiran yin kade-kade.
A Nairobi, babban birnin Kenya, an kama wani mutum ranar Asabar lokacin zaga-zangar neman a inganta rayuwar mutanen da annobar korona ta shafa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Nairobi, babban birnin Kenya, an kama wani mutum ranar Asabar lokacin zaga-zangar neman a inganta rayuwar mutanen da annobar korona ta shafa.
A ranar asabar din ne a Khartoum, babban birnin Sudan mutane suka taru a wurin jana'izar wani makusanci ga hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir wato Zubair Ahmed al-Hassan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar asabar din ne a Khartoum, babban birnin Sudan mutane suka taru a wurin jana'izar wani makusanci ga hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir wato Zubair Ahmed al-Hassan. Ya kasance a tsare yana jiran shari'a kan cin hanci da rashawa
Ranar Alhamis ke nan - wani mutum a Uganda rike da rediyo don sauraron hukuncin kotun ICC na yanke wa Dominic Ongwen, wani soja da ya rikide ya zama dan tawaye hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara 25.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Alhamis ke nan - wani mutum a Uganda rike da rediyo don sauraron hukuncin kotun ICC na yanke wa Dominic Ongwen, wani soja da ya rikide ya zama dan tawaye hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara 25.
Nomuzi Mabena, mawakiya kuma mai aiki a gidan Talbijin a bikin bajekolin kayan kawa a Midrand da ke Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nomuzi Mabena, mawakiya kuma mai aiki a gidan Talbijin a bikin bajekolin kayan kawa a Midrand da ke Afirka ta Kudu.
A ranar Talata an hangi wata ta bayan hasumiyar wani masallaci da ya sha ado saboda watan azumin Ramadana a Alkahira da ke Masar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Talata an hangi wata ta bayan hasumiyar wani masallaci da ya sha ado saboda watan azumin Ramadana a Alkahira da ke Masar.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.