Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Idriss Deby: Hotunan jana'izar tsohon shugaban Chadi da ya mutu bayan gumurzu da 'yan tawaye
A ranar Juma'a ne ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban Chadi Idriss Deby wanda ya mutu a farkon mako sakamakon raunukan da ya ji lokacin fafatawa da mayakan 'yan tawaye.
Shugaba Deby, wanda ya kwashe fiye da shekaru 30 yana mulkin kasar, ya mutu kwana guda bayan sakamakon zabe ya nuna cewa shi ne ya yi nasara inda yake shirin soma mulki a wa'adi na shida.
Dansa Mahamat Idriss Déby Itno wanda aka fi sani da Janar Kaka ne zai jagoranci kasar na watanni 18 zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.
Shugabannin kasashe da dama ne suke halartar jana'izar Mr Deby wadda ake gudanarwa a N'Djamena, babban birnin kasar.