Idriss Deby: Hotunan jana'izar tsohon shugaban Chadi da ya mutu bayan gumurzu da 'yan tawaye

An wallafa

A ranar Juma'a ne ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban Chadi Idriss Deby wanda ya mutu a farkon mako sakamakon raunukan da ya ji lokacin fafatawa da mayakan 'yan tawaye.

Shugaba Deby, wanda ya kwashe fiye da shekaru 30 yana mulkin kasar, ya mutu kwana guda bayan sakamakon zabe ya nuna cewa shi ne ya yi nasara inda yake shirin soma mulki a wa'adi na shida.

Dansa Mahamat Idriss Déby Itno wanda aka fi sani da Janar Kaka ne zai jagoranci kasar na watanni 18 zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.

Shugabannin kasashe da dama ne suke halartar jana'izar Mr Deby wadda ake gudanarwa a N'Djamena, babban birnin kasar.

Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu sojoji dauke da gawar marigayi Shugaba Idriss Deby
Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Janar Mahamat Déby Itno (tsakiya) tare da wasu jami'an gwamnati a wurin jana'izar mahaifinsa.
Hinda Deby

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hinda Deby, mai dakin marigayi Idriss Deby, tana bayani a wajen jana'izar mijinta
Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron (Hagu) ya isa kasar domin halartar jana'izar marigayi Deby
Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Jami'an rundunar sojin Chadi suna sanya ido kan yadda ake gudanar da jana'izar daga wurin da aka kebe musu
Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane sun taru a wajen dandalin da ake gudanar da jana'izar Idriss Deby
Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan jarida na daukar hoton gawar marigayi Idriss Deby wadda ake yi wa jana'iza
Jana'izar Idriss Deby

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tun ranar Alhamis shugaban Nijar (Hagu), da takwaransa na Faransa da Mauritania suka gana a N'Djamena kan shirye-shiryen jana'izar

Karanta labarai masu alaka: