Hotunan Afurka na mako 19-25 Maris 2021: Masoya balan-balan, wasa a cikin ƙanƙara

An wallafa

Wasu daga cikjin ƙayatattun hotunan sassa daban-daban na Afirka:

Wani mutum rike da tarin balan-balan da ake bai wa 'yan uwa da abokan arziki a kofar ofoshin magajin garin Bangui , a jamhuriar tsakiyar Afurka a ranar Lahadi 20 Maris 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana miƙa wa masu halartar wani biki balan-balan a birnin Bangui na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka a ranar Lahadi.
Wata yarinya sanye da takunkumin rufe fuska a ranar farko da dalibai suka koma makaranta bayan shafe watanni su na rufe saboda barkewar annobar cutar korona, a Maputo a Mozambique ranar litinin 22 Maris 2021. .

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata yarinya da ta yi matukar kyau sanye da takunkumi ruwan hoda, lokacin da suka koma makaranta a birnin Maputo na kasar Mozambique, ranar Litinin.
Dalibai sanye da takunkumin rufe fuska da malafa, a cikin ajin daukar karatu a ranar farko da aka bude makarantu a Ruwa, Zimbabwe - ranar Litinin 22 Maris 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Afirka Ta Kudu maƙwabciyar Zimbabwe ma dalibai ne suka koma makaranta a dai ranar Litinin bayan kullen annobar cutar korona.
Yara na wasan kwallon teburi a garin Mopti, da ke gabar teku - ranar Juma'a 19 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yara na wasan kwallon teburi a ranar Juma'a a garin Mopti na kasar Mali, mai iyaka da Jamhuriyar Nijar da kogin Bani.
Mutane na wasan zamiyar kankara a tsaunin Chrea da ke Blinda a - ranar Litin 22 Maris 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yara na jin dadin wasan zamiyar ƙanƙara ranar Litinin a tsaunin Chrea na Algeria.....
Abin zamiyar kankara jere reras, kan kankara a tsaunin Chrea a Blida, Algeria - ranar Litin 22 Maris 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wurin da ake ajiye abin hawa zamiyar kankara, mai nisan kilomita kusan 60 daga kudancin babban birnin kasar, Algiers.
Wani yaro zaune kan kwale-kwalen kamun kifi ya na kallon teku, an dauki hoton bayan rigarsa mai lamba 10 ta dan wasan Barcelona Lionel Messi, a kasar Liberia - ranar Asabar 20 Maris 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mai son kwallon kafa sanye da jesi dauke da lambar dan wasan Barcelona Lionel Messi, zaune a kwale-kwalen kamun kifi a gabar teku a kasar Liberiya ranar Lahadi...
Masunta a cikin kwale-kwalen FC Barcelona a kusa da wurin wasa na Robertsport da ke Grand Cape Mount County, a Liberia - ranar Asabar 20 Maris 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane a cikin kwale-kwalen kamun kifin da aka yi wa kwalliya da tambarin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona....
CYara tsaye gaban ginin da akai wa ado da tambarin kungiyar Barcelona a garin Fanti da ke kusa da wurin wasa na Robertsport a Grand Cape Mount County, da ke Liberia - ranar Asabar 20 Maris 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Duk wani gini ko allo da ke gabar ruwan Lako Piso an yi masa ado da tambarin kungiyar kwallon kafa ta FCB, cikin launuka daban-daban.
'Yar wasan gaba ta Barcelona kuma 'yar Najeriya, Asisat Oshoala tana buga kwallo a lokacin Champions League na mata, da ake karawa tsakanin Barcelona da Manchester a filin wasa na Brianteoda ke birnin Monza,na Italiya ranar Laraba 24 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba, yar wasar gaba ta kungiyar Barcelona kuma 'yar Najeriya Asisat Oshoala, na taimaka wa kungiyarta zura kwallo a ragar Manchester City, a wasan gab da na kusa da na karshen gasar Champions League a kasar Italiya.
Dan wasan tseren keke na Eritrean Merhawi Kudus Ghebremedhinlokacin atisayen shiga gasar tsere ta Volta a Catalunya a kasar Sifaniya, ranar Talata 23 Maris 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gabannin wannan rana, dan wasan tseren keke dan Eritrea, Merhawi Kudus Ghebremedhin ya shiga tseren Volta a Catalunya.
Mace ta na wuce wani gini da aka kawata da launuka ruwan dorawa da da shudo a garin Figuig da ke bakin ruwa a kasar Morocco, mai iyaka da kasar Algeria - ranar Asabar 20 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mace tana wuce wani gini da aka kawata da garin Figuig da ke bakin ruwa a kasar Moroko a ranar Juma'a.
Mace na wucewa ta hanyar da aka yi tsakanin wani gidan kasa, kewaye da bishiyoyin dabino a ranar Asabar 20 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gina garin ne a kusa da gabar ruwa, kewaye da bishiyoyin dabino a kusa da iyakar Moroko da Algeria…
Hoton yadda garin Figuig na Morocco ya ke, hoton ya nuna wasu jakuna uku dauke da kaya a kusa da iyakar Algeria - ranar Asabar 20 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A kwanakin baya an yi zanga-zanga a garin, kan matakin gwamnatin Algeria na korar masu shuka dabino daga yankin da suka dade suna amfani da shi.
Abdul Salam al-Worfali kenan mai kul da horas da dawakai na ba iwa dawakai mnagani a birnin Benghazi, Libya - ranar Litinin 22 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin mai kula da horas da dawakan yankin Larabawa ne yake bai wa daya daga cikin dawakansa magani a birnin Bengazi na kasar Libya.
An harba tanka lokacin bikin yaye wadanda alhakin kula da gabar teku da yankuna masu azrikin man fetur a of Libya - ranar Litinin 22 Maris 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A dai wannan ranar a yammacin kasar Libya, an harba bindigar tankar yaki lokacin bikin yaye wadanda alhakin gadin gabar teku da tsare yanki mai arzikin mai a kasar.
Mutane su na sowa zaune a bayan a kori-kura a lokacin tseren rakuma a kusa da Omdurman, Sudan -ranar Juma'a 19 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yara cikin annashuwa a cikin a kori-kura sun wuce rakuman da ke tsere a kusa da birnin Omdurman na Sudan a ranar Juma'a...
An turke rakuma gabannin gabannin fara tseren a kusa da birnin Omdurman, Sudan - ranar Juma'a 19 Maris 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Iyalai masu kiwon rakuma ne suka shirya tseren rakuman a kauyen al-Ikhlas.
Wasu maza na jira dan cika tukwanen gas a birnin Addis Ababa, Habasha -ranar Juma'a 19 Maris2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai ranar Juma'ar, wasu maza na jira don cika tukwanen gas da za su kai asibiti don taimaka wa 'yan uwansu masu fama da cutar korona, a wani yanki na birnin Addis Ababa a kasar Habasha.
Mai wasan ninkaya Omar Sayed Shaaban sanye da hular roba lokacin atisaye a birnin Akhahira na Masar, eranar Lahadi 21 Maris 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Omar Sayed Shaaban kenan dan kasar Masar mai wasan ninkaya, sanye da hular roba ya na atisaye cikin wani kwamin wanka a birnin Alkhahira ranar Lahadi. A farkon wannan watan ya kafa tarihi a duniya na wanda ya fi kowa yin tsalle mai nisa tare da fadawa cikin ruwa.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.