Hotunan Afrika daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Maris 2021

An wallafa

Wasu zababbun hotunan nahiyar Afrika na wannan makon.

Wasu jakunan dawa a yammacin ranar Lahadi suna tsallakawa titi, tare da tilastawa masu mota dakatawa sai sun tsallaka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu jakunan dawa a yammacin ranar Lahadi suna tsallaka titi tare da tilasta wa masu mota dakatawa sai sun tsallaka
Touré, wani dan kasar Gambian mai kwaso gishiri dauke da kwando a Senegal ranar 16 ga watan Maris 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani dan Gambia mai suna Toure mai sana'ar kwaso gishiri daga kasan kogin Retba a Senegal a ranar Talata
Touré, wani dan kasar Gambian mai kwaso gishiri dauke da kwando a Senegal ranar 16 ga watan Maris 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An fi sanin sa da kogin "Pink Lake" saboda furannin da suke ciki wadanda suke sauya masa launi
Wani zane na kasa mai daukar hankali kan wata matashiya Ansha mai shekara 12 'yar Ethiopia, ranar 15 ga watan Maris 2021

Asalin hoton, Christopher Furlong

Bayanan hoto, A ranar Litinin wasu masu zane sun zana hoton wata yarinya Ansha mai shekara 12 a Habasha.....
Wani zane na kasa mai daukar hankali kan wata matashiya Ansha mai shekara 12 'yar Ethiopia, ranar 15 ga watan Maris 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanen ya matukar daukar ido ya kuma kawata bakin ruwan da aka yi zanen a arewacin Ingila
Wani jami'an tsaro rike da wata mata lullube da tutar algeria a ranar 12 ga watan Maris 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata, wani dan sanda rungume da wata 'yar zanga-zanga, a zanga-zanga mafi tsari da aka yi a Algeriers babban birnin Algeria.
Zanga-zangar da ake yi a al Algiers ta kin jinin gwamnati ce kuma ta samu tagomashi a ranar 16 ga watan Maris 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar na bukatar duk wani mai rike da mukami a gwamnatin kasar ya sauka..
Ranar 15 ga watan 2021. dalibai suka cika titi suna zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar neman tallafi ga daliban jami'a a Johannesburg sun yi cuncurundo a manyan titinan birnin a ranar Litinin.
Wani mutum dauke da kaji a kasuwa ranar 16 ga watan Maris 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na kirga kajinsa a wata kasuwa a Makelle babban birnin yankin Tigray na Habasha a ranar Talata
A ranar 16 ga watan Maris 2021, wani yaro na jika kanshi da ruwa a bakin kogi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A irin wannan ranar a jihar Gedaref da ke gabashin Sudan, wani yaro na jika fuskarsa da ruwa a kogin Atbarah.
Wani mutum na karanta jarida bayan sanar da mutuwar John Nagafuli a ranar Laraba 18 ga watan Maris 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Tanzaniya an wayi gari da Labarin mutuwar shugaban kasar John Magafuli wanda ya mutu yana da shekara 61 a duniya.
People gather for a ceremony organized by Rally of Houphouetists for Democracy and Peace (RHDP) political party in homage to the late Ivory Coast Prime Minister Hamed Bakayoko at the Olympic Stadium in Abidjan, Ivory Coast on March 17, 2021. Hamed Bakayoko, 56, died late Wednesday in Germany after being hospitalized for cancer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, On Wednesday mourners gather at the Olympic stadium in Abidjan, Ivory Coast, to remember the late Ivory Coast Prime Minister Hamed Bakayoko...
Mai kidan rege Alpha Blondy na daga cikin wadanda suka yi waka domin tunawa da marigayin wanda mutu yana da shekara 56 bayan kamuwa da cutar kansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai kidan rege Alpha Blondy na daga cikin wadanda suka yi waka domin tunawa da marigayin wanda mutu yana da shekara 56 bayan kamuwa da cutar kansa
Wata dattijuwa sanye da tufafin da ke dauke da hoton Sarki Zulu wanda ya rasu an dauki hoton ranar 12 ga watan Maris 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu juyayi a Afrika Ta Kudu suna tunawa da Sarki Zulu Zwelithini wanda ya mutu yana da shekara 72 bayan fara da ciwon siga