Gwamnatin Gombe ta naɗa sabon Sarki 'Mai Tangale'

Asalin hoton, Gombe state Govt
Gwamnatin jihar gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta naɗa sabon sarki Mai Tangale na ƙaramar hukumar Ɓilliri.
Malam Danladi Sanusi Maiyamba shi ne ya zama sabon Mai Tangalen kamar yadda wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnatin jihar Isma'ila Uba Misilli ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce Gwamna Inuwa Yahaya ya yanke wannan hukunci ne bisa ikon da dokar masarautu ta Gombe ta 2020 ta ba shi.
Ta kuma ce an naɗa Malam Sanusi ne saboda kyawawan halayensa da kuma cancantarsa, kamar yadda kwamishinan ƙananan hukumomi da masarutu Ibrahim Dasuki Jalo ya fada a yayin da yake miƙawa sabon Mai Tangalen takardar ba shi sarautar.
A makon da ya gaba ne aka tafka rikicin addini a ƙaramar hukumar Ɓilliri kan batun wanda za a naɗa a matsayin sabon Mai Tangale, bayan mutuwar tsohon sarkin Dr Abdu Buba Maisharu II.
Rikicin har sai da ya kai da sanya dokar hana fita ta awa 24 a ƙaramar hukumar Billiri.

Asalin hoton, Gombe state govt






