Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Kurame Ta Duniya: Amfanin dattin kunne ga mutane
Masana kiwon lafiya sun ce matsalar kurmantaka na daga cikin matsalolin da suke kama dan adam tun daga yarinta wasu kuma tana kama su a cikin lokacin kuruciya ko kuma girma.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware irin wannan ranar ta 3 ga watan Maris domin tuna wa da masu irin wannan matsala domin tattaunawa kan matsalolinsu da yadda za a iya taimaka musu.
Kamar yadda masana suka fada wasu kan iya warkewa daga wannan matsala wasu kuma ba su warkewa har karshen rayuwarsu.
Cutar ana kamuwa da ita ne ta hanyoyi biyu, wasu na samunta ta hanyar gado tun suna ciki, idan ya kasance a danginsu a kwai mai wannan matsala za su iya gada, wasu kuma sai sun girma sanadiyyar wasu matsaloli na rayuwa sai su kamu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 5 cikin 100 na adadin mutanen duniya wato kimanin mutum miliyan 466 ne ke fama da matsalar kunne a halin yanzu.
Cikin wannan adadin, miliyan 34 yara ne, sauran kuma manya ne.
Kashi 60 cikin 100 na abubuwan da suke janyo matsalar ji ana iya maganinsu, kamar yadda masana suka bayyana.
BBC ta tattauna da Dakta Magaji Awwal, wani ƙwararren likitan kunne da ke babban Asibitin kula da matsalolin kunne da hanci da kuma maƙogwaro wato ENT a Kaduna.
Likitan ya bayyana wasu abubuwa da dan adam ke yi da suke cutar da lafiyar jin shi ko kuma kunnansa a bisa rashin sani.
Ya ce wannan matsala ta rashin ji na karuwa ne a cikin al'umma, saboda a kiyasin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta ce nan da 2050 masu wannan matsalar za su kai miliyan 900.
Dakta Magaji ya ce "dattin kunne yana da gudun mawar da yake bayarwa a rayuwar dan adam domin kuwa yana da rawa da yake taka wa kamar haka.
"Na farko yana da danƙo ta yadda yake hana ƙura shiga cikin kunnen mutum inda tantanin ji yake, ko ta shiga yana rike ta ya hana ta karasa wa.
"Na biyu yana da wasu suna darai da suke kashe kwayoyin cutar da suke zillewa su shiga kunnen shi yasa a wani lokacin ake ganinsa baki wani lokacin ruwan ƙasa.
"Akwai wari-warin da yake ko in ce kamshi wanda yake hana kwari shiga kunne kuma ko sun shiga suna shakar kamshin suke mutuwa .
"Yana da matukar santsi ta yadda ba ya barin ruwa ya zauna a kunne, a lokuta da yawa in mun je wanka muna bari wura ya shiga kunnenmu, wannan dattin ba ya kyale shi ya karasa can ciki yana kare shi ya kuma koro shi bakin kunne, in ji Dakta Magaji.
Shi wannan dattin kamar mai ne da yake bai wa kunne damar zama cikin danshi, cire shi da tsinke ko wani abu zai iya cutar da kunnen baki daya