Saudiyya : Biden zai tattaunawa da Sarki Salman na Saudiyya

An wallafa

Fadar shugaban Amurika ta White House ta sanar da cewa shugaba Joe Biden na shirin yin wata tattaunawa da sarki Salman na Saudiyya nan ba da jamawa ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ta shirya fitar da rahotonta game da kisan dan jaridar nan na kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi.

Mista Khashoggi mazaunin Amurika an halaka shi ta wata mummunar hanya a cikin karamin ofishin jakadanci Saudiyya dake Santambul a Turkiyya cikin shekarar 2018.

Ana sa ran wannan rahoto dai zai nuna cewa da hannun Saudiya dumu -dumu ba tare da wata tanttama ba a cikin wannan kisa, musamman ma masarautar ta Saudiyya, abun da Sarki Mohammed bin Salman ya musunta tun a baya.

Mista Biden ya sanar da cewa ya na son ya dai-daita hulda da Saudiya .

Sakatariyar watsa labaran fadar White House Jen Psaki, ta sanar da cewa babban jami'in ma'aikatar lekon asiri ta DNI zai fitar da sanarwa a cikin dan kankanin lokaci.

Ana sa ran rahoton zai bayyana cewa da hannun masarautar Saudiyya, musamman ma shi Yarima mai jiran gado a wannan kisa.Mista Biden ya sayar da cewa yana so ya "sake fasalta" dangantaka da Saudiyya, yana mai nuna cewa Amurka za ta fi son hulda kai tsaye da Sarki Salman. Amma wakilin BBC ya ce Yarima mai jiran gado Mohammed yana da farin jini A tsakanin samari 'yan Saudiyya, sannan yana da karfin mafa aji sosai.