Kayatattun hotunan Afirka na mako: Daga 12 zuwa 18 ga watan Fabrairu na 2021

An wallafa

Mun zabo muku fitattun hotunan Afirka na wannan makon:

Wani nau'in zalbe suna cin abinci a cikin Tafkin Magadi da ke kwazazzabon Rift na kasar Kenya ranar Juma'a

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani nau'in zalbe suna cin abinci a cikin Tafkin Magadi da ke kwazazzabon Rift na kasar Kenya ranar Juma'a
A ranar ce wadannan matan masu aikin hakar zinare suka halarci wani biki a kasar Mali...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar ce wadannan matan masu aikin hakar zinare suka halarci wani biki a kasar Mali...
A nan kuma wata mace ce ake yi mata daurin dan kwali a wani bangare na bikin nunin zinare na duniya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma wata mace ce ake yi mata daurin dan kwali a wani bangare na bikin nunin zinare na duniya a kasar Mali.
A man sells roses of various colours from an outdoor stall in Abidjan, Ivory Coast - Friday 12 February 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kazalika ranar Juma'a, wannan mutumin ya jera furannin da yake sayarwa a Abidjan, babban birnin Ivory Coast, gabanin bikin Ranar Masoya ta Duniya, wato Valentine's Day...
Wasu mata suna tattaunawa a yayin da suke kallon furanni a wata kasuwa a Kampala, Uganda

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Irin abin da ya faru ke nan washegari a Kampala, babban birnin Uganda.
A Dandalin Wadanda suka yi shahada da ke Tripoli ranar Laraba, 'yan kasar Libya sun yi bikin cika shekara 10 da soma boren da ya kai ga tumbuke mulkin s mark the 10th anniversary of the Arab Spring, which led to the ousting of Col Kanar Muammar Gaddafi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Dandalin Wadanda suka yi shahada da ke Tripoli ranar Laraba, 'yan kasar Libya sun yi bikin cika shekara 10 da soma boren da ya kai ga tumbuke mulkin Kanar Muammar Gaddafi.
Ranar Juma'a a Gabashin Libya, wani mutum yana shirya dokinsa da yake shirin sayarwa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a a Gabashin Libya, wani mutum yana shirya dokinsa da yake shirin sayarwa
A ranar ce kuma a Oussouye, Senegal, wannan mutumin ya hau kan bishiyar kwakwa domin samo wacce zai murza a yi man ja domin yin girki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar ce kuma a Oussouye, Senegal, wannan mutumin ya hau kan bishiyar kwakwa domin samo wacce zai murza a yi man ja domin yin girki.
A ranar Talata cikin sanyi da ruwan sama, baki sun tsaya a wajen dakunansu da ke otal din Grand Hyatt Grand Nile Tower a Alkahira, babban birnin Masar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Talata cikin sanyi da ruwan sama, baki sun tsaya a wajen dakunansu da ke otal din Grand Hyatt Grand Nile Tower a Alkahira, babban birnin Masar.
Ranar Alhamis, an ga wadannan takamab yashe a makarantar kwana ta Kagara da ke jihar Neja ta Najeriya, washegarin da aka sace dalibai daga makarantar 'Yan bindigar sun kashe mutum daya sannan suka sace mutum 27, a cewar gwamna jihar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Alhamis, an ga wadannan takalman a yashe a makarantar kwana ta Kagara da ke jihar Neja ta Najeriya, washegarin da aka sace dalibai daga makarantar. 'Yan bindigar sun kashe mutum daya sannan suka sace mutum 27, a cewar gwamna jihar.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.