Somaliya: An kai hari kusa da fadar shugaban ƙasa

An wallafa

Gwamnatin Somaliya ta ce wasu mayaƙa sun kai wa sojoji hari a Mogadishu, babban birnin kasar, kusa da Fadar Shugaban Kasa.

A wata gajeriyar sanarwa, Ministan tsaron kasar ya ce an dakile harin.

Mazauna yankin sun ba da rahoton jin ƙarar bindigogi.

Lamarin na zuwa ne sa'o'i kafin jam'iyyun adawa na Somaliya su shirya gudanar da zanga-zangar adawa da Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed da ya ci gaba da kasancewa a kan mukaminsa.

Wa'adinsa ya kare a makon da ya gabata, ba tare da zaɓar wanda zai gaje shi ba, abin da ya jefa Somaliya cikin rikicin siyasa.

Ana sa ran Shugaba Mohamed zai yi wata ganawa tare da shugabannin yanki biyar na Somaliya a zaman wani bangare na kokarin kawo karshen matsalar.

Rikicin Siyasa

Tashin hankali na sake tsanani a Somaliya, a wannan lokacin da tsarin siyasar ƙasar mai rauni ke karan-batta da shirye-shiryen zabukan da ke tafe, akwai batun soma janye dakarunta da Amurka ke yi a wurare masu muhimmanci da kuma damuwar da ake nunawa kan sake ɓullar sabbin ƙungiyoyin jihadi a ƙasar.

Jami'an diflomasiya da masu sa ido sun yi gargadi cewa kasar - wadda ta shafe shekaru 30 babu tsarin gwamnati da taɓarɓarewar lamaru - yanzu haka ta sake daukar hanyar komawa gidan jiya, ƙoƙari da ci gaban da ake samu na sake gina ƙasar na shirin rugujewa.

"Somaliya ta shiga mataki mai muhimmaci," kamar yada wakilin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Jawes Swann ya shaida wa BBC, yana mai gargaɗin cewa "halaye da bijiro da tsarin da ake ganin a ketare" da shugabannin ƙasar da yankunan ke aikatawa - yayin da suke tafka muhawara kan jinkirta zabukan ƴan majalisa - na iya haifar da rikici.

Ƙungiyoyi da hukumomi masu karfi - ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai da wakilan wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika - sun aike da sakon gargadi ga ƴan siyasar Somalia wanda ya bukaci sulhu. "Duk wani yunkuri ko barazanar amfani da salon rikici ba abu ne da za a lamunta ba," a cewar sanarwarsu.