Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AbdulRasheed Bawa: Buhari ya nada shi a matsayin sabon shugaban EFCC
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nada AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati - EFCC.
An nada AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC ne watanni bayan sauke Ibrahim Magu wanda aka zarga da cin hanci.
A wasikar da ya aike wa majalisar dattawan kasar, Shugaba Buhari ya ce AbdulRasheed yana da kwarewa a fannin bincike irin na zamba da almundahana da kuma halatta kudin haramun.
Sanarwar, wadda kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya sanyawa hannu, ta ce AbdulRasheed Bawa, mai shekaru 40, yana da digiri a fannin tattalin arziki da kuma digiri na biyu a fannin harkokin diflomasiyya da harkokin kasar waje.
Ya halarci horo na musamman daban-daban a kasashen duniya, kuma yana cikin wadanda suka soma aiki da EFCC a shekarar 2005.
Idan aka tabbatar da nadin nasa, zai kasance mutum mafi karancin shekaru da ya rike mukamin shugabancin EFCC.
A watan Yulin 2020 ne Shugaba Buhari ya sauke Ibrahim Magu daga kan mukamin bisa zarge-zargen cin hancin da ake yi masa - wadanda ke da alaka da yadda ya tafiyar da kudade da kadarorin da aka kwato daga hannun mutane da hukumomi.
Tun bayan sauke shi ne kuma Mohammed Umar yake rikon mukamin shugaban na EFCC.