Juyin juya halin Masar: 'Yadda hargowar masu zanga-zanga ta razana ni'

An wallafa

Shekaru goma da suka gabata, dandalin Tahrir na tsakiyar Alkahira shi ne matattarar zanga-zangar adawa da Shugaban Masar na wancan lokacin Hosni Mubarak da gwamnatinsa.

Mai daukar hoto Laura El-Tantawy na daya daga cikin wadanda suka dauki bayanan zanga-zangar wacce ta kara girma kuma ta kai ga rikici tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma tsige Mubarak daga mulki.

El-Tantawy ta kasance a Italiya lokacin da aka fara zanga-zangar a babban birnin Masar amma ta ƙuduri aniyar kasancewa duk da sanin haɗarin da za ta fuskanta.

"Na ji tsoro na kasance a wurin ganin yadda rahotannin da nake karantawa kama daga kan na katsewar wutar lantarki, da katse yanar gizo a duk fadin kasar, maharba a saman bene suna harbin masu zanga-zanga da masu daukar hoto da kuma wakilan kafofin watsa labarai.

Amma a ƙarshe, El-Tantawy ta ji cewa wani lokaci ne na tarihi da ta yi adabo da shi.

"Kallon labarai da nake yi a wannan lokaci ne ya sa na ji lallai zan iya yin rashin lokacin da tarihi ba zai manta da shi ba

"Dama na fara daukar bayanan bidiyo na abubuwan dake faruwa a Masar tun daga 2005.

Babu wata tantama naji cewa lallai ya kamata in kasance a dandalin Tahrir don daukar wannan lokacin a matsayin wani bangare na tarihin aikina''.

Lokacin da ta shiga dandalin, El-Tantawy sai ta aminta da kanta, da kuma yiwuwar kasancewa lafiya, ko da yake shiga da fita dandalin ne ke da matukar hadarin gaske, kasancewar akwai ƙungiyoyin da za su saci kyamarori kuma su far wa 'yan jarida.

El-Tantawy ta ce "Na yi wannan hoton ne a ranar 2 ga Fabrairu, 2011,"

"Wannan ba rana ce mara kyau a dandalin Tahrir.

Sai da ya zama ana kallon lamarin a matsyainin baka yi bani guwi, lokacin da magoya bayan Mubarak masu rike da takubba da bulala suka hau dawakai da rakuma zuwa dandalin suka afkawa masu zanga-zangar.

"Rana ce mai radadi da ban tsoro. Na kasance a cikin wata rariya a bayan dandalin ina daukar hoton wadanda suka ji rauni."

Wannan na daya daga cikin sannannun fituntunun da tashin hankali na adawa da Mubarak ya fuskanta, da kuma ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

El-Tantawy ta ce "A koyaushe ina boye kyamara ta a lokacin da zan bar Tahrir,"

"Cikin kankanin lokaci a cikin kwanaki 18 na samu mai daukar hoto da kuma nadar bidiyo, don in ba haka ba koyaushe ina wurin da kaina.

"Yanayin yana canzawa a kowace rana.

"Wuri ne da launin fata, addini, da zamantakewar al'umma basu dami kowa ba. Kowa ya kasance a wurin ne saboda wani dalili.

Ganin hadin kai a wannan wurin ya wuce duk wani bambancin da ke iya faruwa."

El-Tantawy ta yi wannan hoton a ranar 11 ga Fabrairu 2011, ranar da Shugaba Mubarak ya sauka.

"Ya kasance ɗaya daga cikin lokutan da suka fi daukar hankali a matsayina na mai ɗaukar hoto.

"Na yi ƙoƙari don ɗaukar yanayin da mutane ke ciki a wannan lokacin a tarihi.

Sama ta haskaka da wasan wuta kuma rurin jama'a ya rika girgiza ƙasa, kamar yadda na rika ji a ƙarƙashin ƙafafuna.

"Abin da ya kasance tare da ni game da dandalin Tahrir shine yadda jama'a suka bada ransu a wannan lokacin.

"Misirawa mutane ne masu son zuciya, muna duban baya fiye da yadda muke hango ta yanayin rayuwarmu ta da da kuma abin da kakanninmu na tsohuwar Masar suka bar mana.

A dandalin 'Yanci na Tahrir mutane suna kallon gaba tare da fata da buri.

"Wannan wani sabon abu ne a gare ni a Masar, na sa ido fiye da na baya."

Ga mutane da yawa, ba shakka suna tunawa da abubuwa daban daban masu ciwo a ransu da suka faru a wannan dandali.

A ranar 22 ga Fabrairun 2012, El-Tantawy tana cikin 'yan jarida da yawa da suka hallara a wajen makarantar' yan sanda da ke New Cairo suna jiran sanarwar ko za a tuhumi tsohon Shugaba Mubarak da ministansa na cikin gida a lokacin, Habib al-Adly da ba da umarnin harbewa da kashe masu zanga-zanga.

El-Tantawy ta ce "A wannan rana na hadu da Safeya Abdelaziz Mohamed,"

"Danta yana cikin mutane da yawa da suka mutu a lokacin juyin juya halin.

Akwai yanayin amincewa da kaddara, da kuma tsananin bakin ciki a fuskarta.

"Ta sha kuka lokacin da kotu ta sanar da hukuncin da ta yanke wa Mubarak da Adly."

Bayan shekara guda, El-Tantawy ta ɗauki wannan hotuna cikin Yunin 2013, a wata zanga-zanga a dandalin Tahrir da ta sake barkewa.

"A lokacin kafafen watsa labarai na da wani ra'ayi, cewa ba a ba wa mata damar shiga zanga-zangar a dandalin Tahrir ba saboda tasirin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi," wacce dan takararta ya yi nasarar farko a zaben shugaban kasa.

"Wannan bai taɓa faruwa ba a dandalin Tahrir, inda na ga mata suna yaƙi kafada-da-kafada a kan gaba da kuma kula da waɗanda suka ji rauni a wuraren shan magani na wucin gadi.

"Na yi imanin ɗaya daga cikin abubuwan da juyin juya halin ya bari shi ne tasirin da ya bar wa 'yan matan Masar su mallaki makomarsu da yaƙi da ra'ayoyi da al'adun gargajiya da ke cutar da su, kamar cin zarafin mata da kuma ra'ayin addini."

Abubuwan da suka faru a cikin 2011 sun kasance wani muhimmin lokaci a tarihin Misira, amma kuma yana da ma'ana ga El-Tantawy.

"A matsayina na yar kasar Masar, ji nake kamar na rubuta labarin karnina, da gwagwarmayarmu ta ganin mutunci da girmamawa.

"Hakan kuma ya sake tabbatar min da sha'awar daukar hoto da kuma fadawa mutane labarai game da gida.

Tun daga wannan lokacin El-Tantawy ta ci gaba da ƙirƙirar labarai wanda ya samo asali daga abubuwan da ta gani, da kuma rayuwa tsakanin gidaje biyu, ɗaya a Burtaniya, ɗayan a Misira.

Kwanan nan ta buga wani littafinta da ta kwashe shekaru goma tana aiki a kai mai suna (In the Shadow of the Pyramids) wanda ya hada da hotunan da ta dauka na juyin juya halin masar tsakanin 2005 da 2014.

Ta ce "A wannan littafin, hotuna ne na ranakun da aka kama su,"

"Wannan baƙon abu ne a cikin littafin ɗaukar hoto. Yana da mahimmanci a gare ni in girmama shahararrun hotunan yayin da nake tunani a kan canjin juyin juya hali''.