Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ce-ce-ku-ce kan batun rusa gadar Kofar Nasarawa a Kano
Matakin gwamnatin Kano da ke Najeriya na rushe gadar sama ta ƙofar Nasarawa ya janyo ce-ce-ku-ce a jihar.
Gwamnatin Kano ta ce ta yanke shawarar rushe gadar ne saboda ta fara zaizayewa saboda rashin ingancin aiki da aka yi lokacin gina gadar.
Gadar Nasarawa na cikin ayyukan da gwamnatin tsohuwar gwamnatin Kano ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta kashe biliyoyin naira wajen gina manyan gadoji a Kano.
Yanzu kuma gwamnatin Ganduje ta ce ƙwararru na nazari kan gadar da ingancinta kuma za su gabatar da rahoto ga gwamnati kan abin da ya dace. Ko a gyara gadar ko a rushe a yi sabuwa, kamar yadda kwamishinan yaɗa labarai Mallam Muhammad Garba ya shaida wa BBC.
Wannan ya haifar da maharawa da ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan al'ummar inda wasu ke goyon bayan matakin wasu kuma ke suka.
Wasu ƴan jihar na ganin bai kamata a ce an kashe biliyoyin kuɗi an yi gada kuma ba da daɗewa ba wata gwamnati ta ce za ta rushe ta yi sabuwa.
Wasu kuma na ganin idan an gano matsala ba laifi ba ne a rushe gadar domin kaucewa abin da ya taɓa faruwa a Dorayi.
Wani ɓangare na al'ummar Kano kuma na yi wa matakin kallon wata manufar siyasa da yunƙuri na shafe ayyukan tsohuwar gwamnatin Kwankwaso saboda adawa.
Me gwamnatin Kano ta ce?
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya ce dole gwamnati ta ɗauki mataki kan duk abin da ya kasance mai haɗari ne ko kawo illa ga rayukan al'umma.
Ya ce shekara biyu, kwararru na koka wa gwamnatin Kano, kan yadda wasu daga ciki turakun gadar suka fara zaizayewa.
"Kuma yanzu bayan nazari gwamnati ta ga akwai buƙatar a kawo mata shawarar abin da ya kamata ta yi," in shi kwamishinan.
Gwamnatin Kano ta ce yanzu ƙwararru na nazari kan gadar da ingancinta kuma za su gabatar da rahoto ga gwamnati kan abin da ya kamata a yi.
A cewar Malam Garba ana so ne a yi gyara kamar yadda gwamnan Kaduna Malam Nasir Elrufa'i ya rusa gadar da makarfi ya yi a kawo.
Kuma gwamnati tana fatan cikin shekara ɗaya za ta sake fasalin gadar zuwa ta zamani, a cewarsa.
Sannan ya musanata zargin cewar gwamnatinsu na ƙoƙarin shafe ayyukan da tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi ne shi ya sa ta ke shirin daukar wannan mataki.
Masu sharhi kan al'amarun yau da kullum na ganin ba gyara ko sabunta gadar ba ne ya kamata gwamnati ta ba fifiko, da raahin sanin abin da mutane ke ya kamata tayiwa mutanen jahar, wanda suka ce akwai bukatar gwamnatin ta Kano ta sauya tunani.
Sai dai masu sharhi kan alamarun yau da kullum na yi wa matakin gwamnati ta Kano na gyara ko sabunta gadar, da rashin sanin abin da ya kamata ta yi wa mutanen jahar.
Bala Abdullahi Kaugama shugaban gammayar ƙungiyar tabbatar da adalci a Najeriya ta Network for Justice ya ce akwai bukatar gwamnatin ta Kano ta sauya tunani.