Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama alkalin Kotun Ƙoli cikin 'masu yunkurin juyin mulki' a Haiti
Firaministan kasar Haiti ya tuhimi wani alkalin kotun kolin kasar da wasu mutum fiye da ashirin - ciki har da wani babban jami'in 'yan sanda - da kitsa shirin hambarar da gwamnatin shugaban kasar Jovenal Moise.
Firaminista Joseph Jouthe ya kuma ce tuni ake tsare da wanda a ke tuhumar.
Mista Jouthe ya sanar da cewa hukumomin kasar Haiti sun kwace wasu makamai - da su ka hada da bindigogi da harsasai masu dimbin yawa, da kuma kudaden kasar waje.
Ya bukaci wadanda ke da hannu cikin shirin hambare gwamnatin da su bi hanyoyin da doka ta tanada idan su na son karbar mulki ne:
"Muna kira da a zauna lafiya, kuma a hau teburin tattaunawa. Ba na son tashin hankali, domin ba shi da amfani."
Ya kara da cewa, "kamata yayi ku shiga zaben kasa mai zuwa, ku nemi amincewar jama'a kana ku shiga zaben, ta haka ne za ku iya karbar mulki."
Shugabannin jam'iyyun adawar Haiti sun soki kamawa da tsare mutanen da gwamnati ta yi -- wanda ke zuwa a ranar da su ka ce wa'adin shugaban kasar ya zo karshe.
Mista Moise dai ya nace yana da sauran shekara guda kafin ya sauka daga mukamin shugaban kasar, yana cewa shekararsa ta farko ta wucin gadi ce.
Haiti ce kasar da tafi fama da talauci a nahiyar Amurka ta Kudu, inda kashi 60 cikin 100 na 'yan kasar matalauta ne futuk.