Cicely Tyson: Bakar fatar da ta kafa tarihi a fina-finan Hollywood ta rasu tana da shekara 96

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Daya daga cikin matan da suka assasa fina-finan Hollywood Cicely Tyson - wadda ta shahara wajen taka rawa a matsayin Ba'amurkiya 'yar asalin Afirkas - ta rasu tana da shekara 96, a cewar manajanta.

Ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwarta ba. Tsohuwar mai sana'ar tallata kayan kawa ce wadda ta kwashe shekara saba'in tana fitowa a finafinai.

Tyson ya lashe kyautar Emmys sau biyu a rawar da ta taka a wani fim da ke wayar da kan jama'a kan 'yancin mutane mai suna The Autobiography of Miss Jane Pittman da aka fitar a 1974.

Kazalika ta zama mace bakar fata ta farko da ta taka muhimmiyar rawa a wani wasan kwaikwayon talbijin East Side/West Side a shekarun 1960.

Wani abu da ta yi a rayuwarta wanda ya burge masu kallonta shi ne yadda take kin fitowa a matsayin karuwa ko a fina-finan da ake muzanta bakar fata.

A yayin da yake a bai wa Tyson lambar yabo ta the Presidential Medal of Freedom a 2016, tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya ce baya ga nasarorin da ta samu a matsayin 'yar wasan kwaikwaiyo, ta kawo sauyi kan tarihin kasar.

Cicely Tyson ba ta fitowa a fina-finan da ke muzanta mata bakaken fata, kuma tana taka rawa ne kawai a fina-finan da ke da jigo mai kyau.

"Na kwashe fiye da shekara 40 ina aiki da Miss Tyson, kuma ina kallon duk shekara a cikin shekarun nan a matsayin abin alfahari da albarka," in ji manajanta Larry Thompson a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis yana bayyana rasuwarta.

Shahararrun mutane ne suka yi ta bayyana alhininsu a kan rasuwarta.

A sakon ta'aziyyar da ta aike kan mutuwar Cicely Tyson, fitacciyar mai watsa labaran Amurka kuma tauraruwar fina-finai Oprah Winfrey ta ce: "Ta yi amfani da sana'arta wajen haskaka rayuwar bakaken fata. Rawar da ta taka ta yi daidai da abubuwan da ta yi imani a kansu; ba ta taba nuna gazawa ba."