Shagulgula, addu'o'i da kifaye na cikin hotunan Afirka na wannan mako

An wallafa

Hotunan abubuwan da suka faru a Afrika na wannan makon:

Ranar Talata a arewacin Algeria, mata ƴan ƙabilar Berber suka yi bikin Yennaver, wato sabuwar shekararsu inda ake yin sadaka don samun ci gaba da arziki.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Talata a arewacin Algeria, mata ƴan ƙabilar Berber suka yi bikin Yennaver, wato sabuwar shekararsu inda ake yin sadaka don samun ci gaba da arziki
Ranar Juma'a, iyalai sun yi murnar sako sojoji 23 da aka yi zarginsu da kashe tsohon shugaban DR Congo Laurent Kabila shekaru 20 da suka gabata.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a, iyalai sun yi murnar sako sojoji 23 da aka yi zarginsu da kashe tsohon shugaban DR Congo Laurent Kabila shekaru 20 da suka gabata
Wani raƙumi yana kiwo da almuru a gabashin Sudan, kusa da sansanonin 'yan gudun hijira da ke Habasha, ranar Juma'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani raƙumi yana kiwo da almuru a gabashin Sudan, kusa da sansanonin 'yan gudun hijira da ke Habasha, ranar Juma'a.
Wani jirgi mai saukar ungulu na Rasha a kusa da babban birnin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ranar Lahadi, kusa da inda 'yan tawaye ke kai hari. Dakarun Rasha sun daɗe da shiga kasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani jirgi mai saukar ungulu na Rasha a kusa da babban birnin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ranar Lahadi, kusa da inda 'yan tawaye ke kai hari. Dakarun Rasha sun daɗe da shiga kasar.
Duk a rana guda, wani mai fatan wayar da kai ta hanyar sanya kaya masu kama da ƙwayar cutar korona na cikin dubban mutanen da suka shiga tsere a Addis Ababa a Habasha.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Duk a rana guda, wani mai fatan wayar da kai ta hanyar sanya kaya masu kama da ƙwayar cutar korona na cikin dubban mutanen da suka shiga tsere a Addis Ababa a Habasha.
Ana na yi wa 'yan Uganda gargaɗi kar su ci kifayen da suka mutu da suka tsinta a bakin tabkin Victoria. Jami'ai na ci gaba da bincike, amma sun ce wani nau'in kifi na Nile Perch ne kawai abin ya shafa kuma mai yiwuwa mutuwar tasu na da alaƙa da raguwar sinadarin oxygen.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana na yi wa 'yan Uganda gargaɗi kar su ci kifayen da suka mutu da suka tsinta a bakin tabkin Victoria. Jami'ai na ci gaba da bincike, amma sun ce wani nau'in kifi na Nile Perch ne kawai abin ya shafa kuma mai yiwuwa mutuwar tasu na da alaƙa da raguwar sinadarin oxygen.
Wani mutum na wucewa ta gaban zanen wani mai kaɗa kuri'a, kwana guda kafin zaɓe a Uganda.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum na wucewa ta gaban zanen wani mai kaɗa kuri'a, kwana guda kafin zaɓe a Uganda.
Wasu matasa na nishaɗi da ɗebe kewa a Cairo, babban birnin Masar ranar Asabar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu matasa na nishaɗi da ɗebe kewa a Cairo, babban birnin Masar ranar Asabar.
Annobar korona ta sa an hana taron jama'a kuma hakan na nufin masu yawon byɗe ido ƴan ƙalilan ne suka halarci bikin Vodun na shekara shelara a Benin ranar Lahadi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Annobar korona ta sa an hana taron jama'a kuma hakan na nufin masu yawon byɗe ido ƴan ƙalilan ne suka halarci bikin Vodun na shekara shelara a Benin ranar Lahadi.
Haka kuma, ranar Talata wani yaro ya dauki robobi don ɗebo ruwa a wani masallaci a dakar, babban birnin Senegal.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haka kuma, ranar Talata wani yaro ya dauki robobi don ɗebo ruwa a wani masallaci a dakar, babban birnin Senegal.

Dukkan hotunan nan suna da hakkin mallaka.