Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya za ta gina birnin da babu titi da mota
Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Mohammed bin Salman ya sanar da wani tsari na gina sabon birni da za a yi a nan gaba a arewa maso yammacin kasar.
Ibn Salman ya yi hasashen gina birnin ne ta hanyar wani tsari da ya saba da tunanin yadda aka saba gina birane.
Za a yi wa birnin lakabi da 'The Line' kuma zai zama mai tsawon kilomita 170.
To sai dai ba kamar yadda aka saba gani ba, shi wannan birnin ba shi tituna ballantana ababan hawa su hau har su fitar da hayakin da ke gurbata muhalli.
Hanyar sufuri ga jama'a a birnin da ma dakon kaya za su kasance a karkashin kasa.
Wannan birnin dai zai kasance wani bangare na katafaren birnin da Saudiyyar ta ambaci gina shi a kasar a baya-bayan nan a shirinta na fadada hanyoyin samun kudin shiga.
Dukkan tsare-tsaren Saudiyyar da suka shafi yawon bude ido da gine-gine na ta'allake da shirin gina katafaren birnin da wasu ke yi wa kallon mafarki.