Alban Bagbin: Abubuwan da ya kamata ku sani kan sabon Kakakin Majalisar Ghana

Ghana Speaker of Parliament

Asalin hoton, Facebook

An wallafa

An rantsar da Alban Bagbin na jam'iyyar adawa ta NDC a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Ghana, biyo bayan rikicin da ya ɓarke yayin zaben wanda zai riƙe matsayin.

A cikin daren Laraba ne aka girke sojoji a cikin ginin majalisar domin kwantar da hankali bayan rikicin da ya barke tsakanin mabobin jam'iyyun NDC da NPP.

A gefe ɗaya kuma wani ɗan majalisa da ya ɗauke takardun zaɓen ya tsere daga cikin ginin da su.

A makon da ya gabata ne jam'iyyar NDC ta shigar da koke kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasar kan ta yi watsi da nasarar da Shugaba Nana Akufo Addo ya samu.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Alban Bagbin

  • An haifi Alban Bagbin a ranar 24 ga watan Satumban 1957 a garin Sombo da ke yankin Upper West
  • Mista Bagbin ya halarci jami'ar Ghana daga 1977 zuwa 1980, inda kuma ya je makarantar horas da lauyoyi daga 1980 zuwa 1982
  • Mista Alban ya samu digiri na biyu a ɓangaren gudanar da gwamnati da jagoranci daga wata cibiya a ƙasar ta Ghana da ake kira Institute of Management and Public Administration (GIMPA)
  • Honourable Bagbin ya riƙe muƙamai daban-daban a majalisar ƙasar tun daga 1994
  • Tun daga 1995 zuwa yanzu, Bagbin ya kasance a wata ƙungiya mai suna Parliamentarians for Global Action (PGA), wadda ƙungiya ce mai zaman kanta ta ƴan majalisa daga sassan duniya, kuma mamba ne a ƙungiyar lauyoyi ta International Law and Human Rights Programme
  • Mista Bagbin ya taɓa zama shugaban masu rinjaye a majalisar ƙasar
  • Ya kuma taɓa zama ministan kiwon lafiya na ƙasar har zuwa 2013 inda daga baya Hanny-Sherry Ayittey ya karɓa kujerar
  • Alban Bagbin na da mata guda, Alice Adjua Yornas, kuma ma'akaciya ce a Asusun Kula Da Ƙananan Yara Na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) a ofishin hukumar da ke Ghana