Matsalar Fyaɗe: Yadda ƴar shekara 12 ta tsinci kanta cikin ƙunci
Matsalar fyaɗe na ci gaba da zama gagarumar matsala a Najeriya, inda kusan a kullum sai an samu labarin fyade - wasu lokutan ma ga ƙananan yara.
A watan Yunin bara ne illahirin gwamnonin jihohin ƙasar 36 suka ayyana dokar ta-baci a kan fyaɗe, wadda ta kai ga wasu jihohi sun tsaurara dokokinsu na yaƙi da matsalar.
Ga alama dai jihar da ta fi jan hankali ita ce Kaduna da ke arewacin ƙasar - saboda dokar da gwamnatin jihar ta kafa a watan Satumba ta dandaƙe duk wanda aka samu da laifin yi wa yaro ko yarinya fyaɗe da nufin daƙile matsalar.
A hirar da BBC ta yi da wani da yake yaya ga wata yarinya ƴar shekara 12 da ake zargi wasu maza 10 ne suka yi mata fyaɗe har ta kai ta kamu da ciwon sanyi, yayan ya bayyana yadda wannan ta'annatin da aka yi wa ƙanwar tasa ya jefa rayuwarta cikin baƙin ciki.
"Sun cutar da rayuwar yarinya kuma sun cutar da mu, lalle abin nan ya yi matuƙar ɓata mana rai, ya yi matuƙar mana ciwo, sai ka same ta ta zauna ta yi shiru tana tunani, da munsanta da kuzari da walwala da yawan wasa cikin ƴan uwanta yara, amma yanzu duk ta rage" in ji yayan yarinyar.
A cewarsa, fatan iyali da dangin yarinyar a kullum shi ne a hukunta waɗanda suka aikata fyaɗen dai-dai da dokar dandaƙa da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa.
A wasu lokutan hukumomi na kama waɗanda suke da hannu a lamarin tare da kai su kotu domin hukunta su amma rashin kai rahoton fyaɗen ga hukumomi da rashin hukunta su cikin hanzari, da ƙyama da tsangwama da waɗanda aka yi wa fyaɗen ke shiga na daga cikin ƙalubalen da ake ci gaba da fuskanta a ƙoƙarin yaƙi da fyaɗen da ake kallo a matsayin annoba.
Suma masu fafutuka da kare haƙƙin mata na nuna damuwa da waɗan nan matsaloli - Hajiya Rabi Salisu Ibrahim na daga cikin masu fafutukar yaƙi da fyaɗe kuma ta shaida wa BBC cewa "duk wanda ya yi fyaɗe, ya kashe wanda ya yi wa fyaɗe ne da rai".
A cewar Hajiya Rabi. matsalar fyaɗen ta wuce a riƙa sauya doka ko yin sabuwar doka inda ta ce akwai buƙatar a ɗauki ƙarin matakai wajen aiwatar da dokokin yaƙi da matsalar da hanzarta tsarin gabatar da shaida.













