Trump ya haramta wa Amurkawa amfani da Alipay da wasu manhajojin China bakwai

Alipay sign

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa da za ta haramtawa Amurkawa amfani da wasu manhajojin China takwas,

manhajojin sun hada da Alipay, wadda ake amfani da ita wajen biyan kudade ta intanet a China da kasashe masu yawa. Akwai kuma QQ Wallet da WeChat Pay.

Wannan dokar wadda za ta fara aiki nan da kwana 45, na cewa an haramta amfani da manhajojin ne saboda suna barazana ga tsaron Amurka.

Ta kuma ce ana iya amfani da manhajojin wajen naɗan bayanai kan Amurkawa musamman ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Tencent QQ, CamScanner, SHAREit, VMate da WPS Office na cikin manhajojin da aka haramta amfani da su a Amurka, amma a lokacin Mista Trump ya riga ya bar aiki.

"Tilas ne Amurka ta rika daukan matakai cikin sauri kan wadanda ke hadawa ko ke sarrafa manhajojin kasar China domin mu kare tsaron kasar mu," inji bayanin da dokar ta kunsa.

A baya shugaba Trump ya sanya hannu kan dokokin shugaban kasa irin wadannan kan kamfanoni ko kayayyakin China, inda yake cewa suna iya aikawa da bayanan sirrri ga gwamnatin China.

A watan Agusta, Amurka ta ba kamfanin ByteDance, wanda ya mallaki manhajar nana mai farin jini ta TikTok cews ko dai ya sayar wa Amurka bangaren kamfanin da ke Amurka ko kuma ya bar kasar gaba daya.

Amma duk da cewa kamfanin bai cika ko da daya daga ciin sharuddan da aka gindaya ma sa ba, har yanzu Amurkar ba ta dauki wani matak kan kamfanin ba.