Koriya Ta Kudu: Masu mutuwa sun zarta jariran da ake haifa a ƙasar

Asalin hoton, AFP
Adadin mutanen da suka mutu ya ɗara adadin jariran da aka haifa a Koriya Ta Kudu a 2020, ƙididdiga ta farko makamanciyar hakan da aka taɓa gani a ƙasar.
Wannan lamari ya tashi hankalin ƴan ƙasar, inda da ma ƙasar ke fama da ƙarancin haihuwar jarirai.
Jariri 275,800 kacal aka haifa a ƙasar a shekarar da ta gabata, inda adadin ya sake raguwa da kashi 10 cikin 100 idan aka kwatanta da 2019. An samu mutum 307,764 da suka mutu a bara a ƙasar.
Wannan adadin ya ja hankalin ministan harkokin cikin gida, inda ya yi kira da a kawo sauye-sauye kan wasu tsare-tsare a ƙasar.
Raguwar adadin ƴan ƙasar zai saka ƙasar cikin matsin lamba.
Baya ga ƙaruwar ƙarin matsin lamba kan kashe kuɗin ƙasar sakamakon ƙaruwar buƙata a ɓangaren kiwon lafiya da fansho, raguwar matasa majiya ƙarfi za ta kawo naƙasu ga ayyukan yi a ƙasar wanda hakan kai-tsaye zai kawo cikas ga tattalin arziƙin ƙasar.

Asalin hoton, AFP
A watan da ya gabata, Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in ya ƙaddamar da sabbin tsare-tsare da yunƙurin magance matsalar ƙarancin haihuwa a ƙasar, ciki har da bayar da tallafin kuɗi ga wasu iyalan.
Ƙarƙashin wannan tsari, duk yaron da aka haifa a ƙasar daga shekarar 2022 zai samu garaɓasar kusan dala 1,850, inda hakan zai taimaka wa iyayen su rage zafi kan kuɗaɗen da suka kashe, baya ga wasu kuɗaɗe na wata-wata da za a ci gaba da biyan iyayen har sai jaririn ya cika shekara ɗaya.

Me ya jawo aka samu ƙarancin haihuwa a Koriya Ta Kudu?
Sharhi daga Julie Yoon, BBC Korean

Asalin hoton, EPA
Kusan babban dalilin da ke sa hakan shi ne, matan ƙasar da dama na ƙoƙarin goggayya da maza a wuraren aiki da sauran abubuwa.
Hyun-yu Kim na ɗaya daga cikin irin waɗannan matan. Ita ce babba a gidansu, inda take da ƙanne huɗu, kuma ta bayyana cewa tana da burin samun iyalai sosai. Sai dai tana fuskantar ƙalubalae da dama a ƙasar da ba za su bari ta iya haihuwa ba, amma ta ce za ta sake tunani domin tana so ta samu yara.
Ba ta daɗe da samun aiki ba, kuma ta nuna damuwa ƙwarai kan ɗaukar hutun haihuwa a wurin aikinta.
"Mutane na ce mani ya fi kyau na fara gina kaina a wurin aiki tukuna," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Kuɗin gidaje na daga cikin abubuwan da ke jawo wannan matsala. Ms Kim ta bayyana tsadar gidajen a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke sanyaya wa masu son yin aure gwiwa.
"Idan kana so ka samu yara, ya zama dole mutum ya mallaki gidansa. Amma hakan ya zama abu mai wuya a Koriya."
Sai dai Ms Kim ɗin ta ce ba ta gamsu da tallafin da gwamnatin ƙasar za ta ba ma'aurata ba.
"Kula da yaro na da tsada. Idan gwamnati za ta taimaki mutum da wasu dubban kuɗaɗe hakan ba zai warware matsalar ba."











