Zaɓaɓɓun hotunan Afirka na shekarar 2020

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotunan Afirka na shekarar 2020.

Short presentational grey line
Samburu men attempt to fend-off a swarm of desert locusts flying over a grazing land in Lemasulani village, Samburu County, Kenya - 17 January 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A cikin watan Janairu, dandazon farin dango sun bai wa mutane mamaki a yankin Gabashin Afirka, da ya hada da wadannan mutanen daga kabilar Samburu a kasar Kenya.
Short presentational grey line
A man in Ethiopia's Mekelle city rides a horse painted in the colours of the Tigray regional flag - 19 February 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A cikin watan Fabrairu, launukan an rika ganin launukan yankin Tigray, na kasar Ethiopia, a ko ina a birnin Mekelle - har a kan dukuna - don murnar cika shekaru 45 da kaddamar da aikin soji kan gwamnatin akidar Makisanci .Daga bisani a cikin shekarar, rikici ya barke a yankin..
Short presentational grey line
Gonzaga Yiga, a 49-year-old community chairperson, appeals to residents - Tuesday 24 March 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yayin da annobar cutar korona ta barke a fadin duniya cikin watan Maris, wani dan kasar Ugandas, Gonzaga Yiga Uganda, ya dauri aniyar fadakar da mazauna Kampala babban birnin kasar tgame da matakan kariya daga yaduwar cutar.
Short presentational grey line
A child has her hair threaded in a salon in Kenya's capital, Nairobi - 29 April 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An fi mayar da hankali sosai kan annobar korona a cikin shekarar, A kasar Kenya, ana iya ganin yadda a cikin watan Afrilu yadda aka mayar da sunan wani wajen gyaran gashi a birnin Nairobi, "coronavirus" saboda yadda za ka ga fasalin kitson na kama da yadda ake gani kwayar cutar a karkashin madubin ganin kwayoyin cuta.
Short presentational grey line
Children in face masks crouch in white circles put at bus stations to ensure social distancing in Kigali, Rwanda -4 May 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Zuwa cikin watan Mayu saka takunkumin rufe fuska ya zama ruwan dare - kuma a Kigali babban birnin kasar Rwanda, wadannan kananan yaran na zana da'ira a kusa da wurin shiga motar haya don karfafa guiwar yin nesa da juna.
Short presentational grey line
An aerial view of a mass gathering of Malians at Independence Square in Bamako -5 June 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A cikin watan Yuni, masu zan ga-zanga sun hallara suna neman hambarar da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta. An kuma yi masa juyin Mulki watanni biyu bayan haka.
Short presentational grey line
A young sheep farmer drags one of his sheep toward the sea in order to clean it in Dakar, Senegal - 28 July 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Muslumai a fadin Africa csun gudanar da bikin Babbar Sallar a cikin watan Yuli. Masu kiwon dabbobi kamar wannan yaron a Dakar babban birnin kasar Senegal, hakan na nufin sai ya wanke tunkiyar kafin ya kai ta
Short presentational grey line
Tanzanian small-scale miner Saniniu Kuryan Laizer poses with two of the biggest of the country's precious gemstones, Tanzanite, as a millionaire during the ceremony for his historical discovery in Manyara, northern Tanzania 24 June, 2020.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani dan kasar Tanzania mai karamar sana'ar hakar ma'adinai, da dare daya ya zama attajiri a cikin watan Yuni sakamakon sayar da da wasu duwatsu n kasar ta Tanzania masu daraja da kudinsu ya kai darajar kusan Dala miliyan uku da rabi, ya sake sayar da wani dutsen a kan Dala miliyan biyu cikin watan Agusta.
Short presentational grey line
A gorilla from the Nyakamwe family holds her newly born twin babies at the Virunga National Park in the Democratic Republic of Congo in this picture released on 22 September 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata goggon biri a gandun dajin Virunga a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na shayar da jariranta a cikin watan Satumba. Nau'in goggon birin da ke daf da bacewa daga doron kasa daya daga cikin takwas da suka yi saura a wannan gandun dajin kenan.
Short presentational grey line
A demonstrator stands atop a vehicle and shouts slogans as others carry banners while blocking a road leading to the airport, during a protest over alleged police brutality, in Lagos, Nigeria - 12 October 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zanga-zangar nuna kin jinin rundunar musamman ta 'yan sanda masu yaki da fashi da makami SARS da aka gudanar a birnn Lagos, da fadin Najeriya, don nuna kin jinin cin zalin 'yan sanda a cikin watan Oktoba, ta haifar da rushe rundunar ta SARS a kasar.
Short presentational grey line
Ethiopian refugees who fled the Ethiopia's Tigray conflict watch the sunset on a hill at the Um Raquba refugee camp in Sudan's eastern Gedaref state - 12 December 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A cikin watan Nuwamba, dubban mutane daga yankin Tigray na kasar Ethiopia suka tsere ta kan iyakar kasar Sudan. Nan ana iya ganin wasu daga cikinsu, makonni kadan a kan dutse a sansanin 'yan gudun hijira na Um Raquba.
Short presentational grey line
A wedding group seen by the beach in Durban, South Africa - 9 December 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana daukar hotuna biki na mutum bibbiyu a birnin Durban na kudancin Afirka Ta Kudu a cikin watan Disamba, bayan da hukumomi suka haramta yin ninkaya a bakin tekun da jama'a ke taruwa saboda sabuwar barkewar annobar korona.

Images from AFP, Getty Images and Reuters