Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhammadu Buhari: Majalisa ta ce ba ta nemi afuwar shugaban ƙasa kan gayyatarsa ba
Majalisar wakilan Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta nemi afuwar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari kan gayyatarsa da ƴan majalisar suka yi don ya je ya yi bayani kan matsalar tsaron da ƙasar ke ciki.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar wanda shi ne mai magana da yawun ƴan majalisar, Benjamin Kalu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai suka fitar cewa ƴan majalisar za su roƙi shugaban ƙasar bayan da suka amince da ƙudurin da ƴan majalisa daga jihar Borno suka gabatar na gayyatar shugaban ƙasar don ya yi wa ƙasa jawabi kan matsalar rashin tsaron da ake fama da shi, ba gaskiya ba ne.
A ranar 1 ga watan Disamba ne ƴan majalisar suka yanke shawarar gayyatar Shugaba Buhari don ya je ya yi musu bayanin halin rashin tsaro da ake ciki a ƙasar, amma sai shugaban bai je ba.
Ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka gabatar da batun halin rashin tsaron da ake ciki inda suka buƙaci gwamnati ta sanya dokar ta ɓaci tare da gayyatar Shugaba Buhari majalisar don ya yi bayani kan yadda zai magance matsalar.
Sannan sun kuma yi magana kan yadda mayaƙan Boko Haram suka kashe wasu manoman shinkafa 43 "kamar kaji" a Bornon.
Bayan da da fari shugaban ƙasar ya amince da gayyatar, sai Ministan Shari'a Abubakar Malami ya ce ƴan majalisar ba su da hurumin gayyatar shugaban ƙasa don ya yi musu bayani.
Ya ce bai kamata shugaban ƙasa ya yi bayani kan matsalar rashin tsaro ba a bayyane kuma majalisa na yin abubuwan da suka saɓa wa kundin tsarin mulki.
A cikin sanarwar Mista Kalu ya ce: "Majalisa ba ta nemi afuwar kowa ba, ta sauke alhakin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata ne a ƙarƙashin jagorancin Shugabanta Femi Gbajabiamila, kuma ba ta wani abu da ya kauce wa kundin tsarin mulki ko wanda zai lalata dimokraɗiyya.