Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Akwai yiwuwar kai hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimeti a Najeriya - DSS
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta gargaɗi ƴan ƙasar da su yi taka tsan-tsan a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara don akwai yiwuwar kai hare-hare.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Talata da daddare mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta Peter Afunanya.
"Hukumar DSS na son sanar da jama'a kan wasu shirye-shiryen wasu miyagu na kai hare-hare muhimman wuraren taruwar jama'a a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara," a cewar sanarwar.
Mr Afunanya ya ce hare-haren da ake tsammanin za su faru ɗin wani shiri ne na miyagu don yi wa gwamnatin tarayya zagon ƙasa.
Waɗanne irin hare-hare za a kai?
Sanarwar ta DSS ta ce munanan hare-haren da aka shirya kai wa za a yi su ne ta hanyar tayar da bama-bamai da hare-haren ƙunar baƙin wake da na sauran munanan makamai.
"Maƙasudin hakan shi ne don a sanya tsoro a tsakanin mutane da kuma yi wa gwamnatin tarayya zagon ƙasa." in ji sanarwar.
Mista Afunanya ya kuma yi kira ga al'umma da su dinga kaffa-kaffa da sa kula ta ɓangaren tsaro sannan su kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba a yankunansu.
Wane mataki DSS ke dauka kan hakan?
Hukumar shawarci mutane da su sanar da duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro ba tare da ɓata lokaci ba.
Sannan hukumar DSS ta ja kunnen masu shirya jawo tashin hankali da rusa zaman lafiyar jama'a da su guji yin hakan "domin kuwa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gurfanar da duk wanda ta kama da laifi a gaban ƙuliya."
"Sannan muna haɗa kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an ɗauki matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin jama'a," in ji sanarwar.
Kana DSS ta bayar da wasu lambobin waya na gaggawa da za a kira idan wani abu ya faru kamar haka; *08132222105* da *09030002189*.
Kuma hukumar ta ce ta yi amfai da wannan damar ta buɗe shafinta na intanet *www.dss.gov.ng* don inganta harkar sadarwa tsakaninta da al'umma.
"Muna kira ga kowa da kowa da su yi amfani da wannan damar ta amfani da hanyoyin da muka bayar wajen tuntuɓarmu kan duk wasu bayanai masu muhimmanci.
Kusan za a iya cewa a yanzu ana zaman ɗar-ɗar ne a mafi yawan yankuna a Najeriya ko dai don tsoron masu satar mutane ko ƴan fashi ko kuma hare-haren ƙungiyar Boko Haram.
Sannan a baya ma hukumar ta DSS ta sha fitar da ire-iren wannan sanarwa a lokutan bukukuwa na addini a ƙasar.