Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Nijar: Shin za a je zagaye na biyu a wannan karon?
A Jamhuriyar Nijar, bisa al`ada, ba a kammala zaɓen shugaban ƙasa sai an kai zagaye na biyu.
Sai dai a wannan karon, jam`iyyar PNDS mai mulki ta sha alwashin cewa za ta yi wa zaɓen kwab daya.
Amma jam`iyyun hamayya sun ce wannan iƙirarin na PNDS ba mai yiwuwa bane.
A yanzu dai za a iya cewa aski ya zo gaban-gosh, kasancewar ana gab da yin zaɓen shugaban kasa. Kuma dukkan `yan dantakara sun duƙufa wajen yakin neman zaɓe, inda suke baje-kolin iyawarsu wajen luguden kalamai da hikima da balagar harshe, kamar Hausa da sauran harsunan ƙasar daga abin da ya sawwaƙa.
Bisa al`adar zaɓe, tun komawar Jamhuriyar Nijar kan turbar dimokuraɗiyya, ba a taɓa samun jam`iyya ɗaya tilo ta yi nasarar kafa gwamnati a zagayen farko na zaɓe ba, sai an shiga zagaye na biyu, a zagaye na biyun ma tare da yin ƙawance da wasu jam`iyyu takwarorinta.
Sai dai a wannan karon, Jam`iyyar PNDS Tarayya, mai mulki na cewa jikinta ya ba ta cewa za ta yi wa zaɓen kwab daya, saboda rawar-ganin da ta yi, da kuma sakacin da abokan hamayyarta suka yi, har kasuwar siyasar ta ci ta watse.
Alhaji Hafizu na Malam Bashir, jigo ne a jam`iyyar inda ya shaida wa BBC cewa da alamu wannan ne karo na farko da ɗan takarar shugaban ƙasa zai kai labari tun a zagayen farko, kuma a cewarsa, ɗan jam'iyyarsu ta PNDS ne zai kai labarin.
"Ƴan adawan Nijar waɗanda su ne ya kamata a ce sun taka wa jam'iyya mai mulki burki, ba su yi tanadi ba, yadda za su taka mai burkin da sai an je zagaye na biyu tukun a samu wanda zai yi shugabancin ƙasa," in ji shi.
Amma jam`iyyun hamayya a nasu ɓangaren, sun ce maganar da jam`iyya mai mulkin ke yi almara ce kawai. Honourable Abdurrahim Balarabe, shi ne kakakin Jam`iyyar RDR, Tcanji na jihar Damagaram kuma ya shaida cewa Jam'iyyar PNDS ba ta isa ta yi kwab ɗaya ba a Nijar.
"In dai jama'ar Nijar ke zaɓe, na yi imani babu zancen kwab ɗaya, idan kuma akwai kwab ɗaya, sai dai mu yi musu kwab ɗaya," in ji shi.
Sai dai masana siyasa irin su Dakta Gambo Alhaji Sani, na ganin cewa komai ka iya faruwa inda ya ce rashin takarar Hamma Amadou wadda ta karya gwiwar magoya bayansa kan iya saka mutane da dama su ƙi fitwa zaɓe.
A wani ɓangaren kuma, ya ce ba lallai bane a yi kwab ɗaya domin kullum a harkar siyasa ana samun ba zata.
`Yan takara talatin ne ke zawarcin kujerar shugaban ƙasar, kuma kowanne na cewa sai inda karfinsa ya kare!