Zaben Uganda: Labaran kanzon kurege game da Joe Biden da sauransu

An wallafa

Yayin da zabukan kasar Uganda ke karatowa a watan Janairu, akwai labaran kanzon kurege masu yawa da ake yadawa yayin da ake zazzafan yakin neman zabe wanda kuma aka sami tashin hankali.

Shugaba Yoweri Museveni, wanda ya ke kan karagar mulki tun 1986 na fuskantar kalubalae daga 'yan takara 11, cikinsu akwai wani matashin mawaki mai suna Bobi Wine.

Wasu daga cikin labaran da ake yadawa sun kunshi labaran karya, a wasu lokutan ma ana sauya ma'anar labarai domin batar da gaskiya.

Joe Biden ba ya goyon bayan 'yan adawa

Misali na farko shi ne na wani bidiyo da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta wanda a ciki aka nuna zababben shugaban Amurka Joe Biden yana kira da a sako Bobi Wine (wanda sunansa na ainihi Robert Kyagulanyi).

Wasu ma na cewa Mista Biden na yi wa Mista Bobi kamfe ne.

A bidiyon ana iya ganin wani mutum mai farin gashi yana cewa: "Dukkanmu mun damu da 'yancin gudanar da addininmu. Muna wuri guda, muna bukatar dimokradiyya a Uganda."

Sai dai mutumin da ke magana ba Joe Biden ne ba, kuma bidiyon shekarunsa biyu.

Bincikenmu ya tabbatar cewa ya fito ne yayin wani gangami da masu adawa da gwamnati suka yi a biranen duniya yayin da aka kama kuma aka tsare Bobi Wine a Agustan 2018.

An gudanar da wannan gangamin ne a Boston, kuma mai magana shi ne Nick Carter, wani dan jam'iyyar Democrat da ke takara a zaben jihar.

Mun kuma tambayi ofishin Mista Biden na zabe, kuma suna sanar da mu cewa "Zababben shugaban kasa bai fitar da wani sako ba ko da ta Twitter kan batun na zabukan Uganda."

Shi ma Barack Obama bai bi sahu ba

A watan jiya tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya fara bayyana cikin wasu bayanai da 'yan adawan Uganada ke rabawa a shafukan sada zumunta.

Mr Obama can be seen in posts with the hashtag #FreeBobiWine, apparently under his own Twitter handle.

But there's no record of Mr Obama posting such a comment on that day, despite the screenshot indicating the tweet got nearly a million re-tweets.

Sakon kuma mna dauke da kuskuen sunan wayar hannu ta iPhone, inda aka rubuta bakin farko da babban baki ba karami ba.

Wannan ba samfurin takardar zabe ba ce

Akwai kuma wani sakon dauke da abin da yayi kama da kuri'ar zabe na 'yan takarar da aka sahale mu su su tsaya takarar mukamin shugaban kasa da alamun jam'iyyarsu.

Amma hukumar zaben kasar ta ce wannan takardar ba ita ce za a yi amfani da ita ba.

Akwai alamu baro-baro da za a iya gani takardar kuri'ar ta bogi ce.

A zabukan da aka yi a baya, ana saka sunayen 'yan takara ne a bangaren hagu, hotunansu da alamun jam'iyyarsu kuma na tsakiya, inda adama ka bat wurin da mai zabe zai dangwala babban dan yatsansa.

Hukumar zaben Uganda ta ce wannan kuri'ar ta bogi ce domin an wallafa sunaye da hotunan 'yan takarar da ba na gaske ne ba.