Abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya wuce
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
Yayin da muke shirin shiga sabon mako, BBC Hausa ta lalubo muku wasu muhimman labarai da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi, wasu daga cikinsu na daɗi wasu kuwa na akasin haka.
Lahadi: Buhari ya kori shugaban hukumar Neja-Delta daga aiki

Wataƙila masu bibiyarmu su iya tuna Kemebradikumo Pondei, shugaban hukumar raya yankin Naija Delta, wanda kwanakin baya ya yanke jiki yayin da kwamitin majalisar wakilan Njeriya ke tsaka da yi masa tambayoyi dangane da ɓacewar wasu maƙudan kuɗaɗe a hukumar da yake jagoranta.
To a ranar Lahadi 13 ga watan Disamba ne shugaba Muhammadu Buhari ya kore shi daga bakin aiki sakamakon zarge-zargen da suka dabaibaye jagorancinsa
Sanarwar da mai taimaka wa Buhari kan kafofin yaɗa labarai, Femi Adesina, ya fitar ta ce an naɗa daraktan kuɗi na hukumar mai suna Effiong Awa a matsayin sabon shugaba.
"Wannan mataki ya zama wajibi sakamakon umarni daban-daban daga wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar kan kwamitin riƙo na shugabancin hukumar NDDC," a cewar sanarwar.
Ɗaliban Najeriya a ƙasashen waje da suka samu tallafin karatu ta hannun hukumar sun yi ƙorafi kan yadda aka yi wancakali da su da kuma sauran zarge-zargen cin hanci da rashawa a kan farfesan.
Litinin: Ranar da aka gano wurin da Ɗaliban GSS Ƙanƙara da aka sace suke

Asalin hoton, @GovernorMasari
A ranar Litinin 14 ga watan Disamba ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun gano wurin da ɗaliban makarantar Ƙanƙara da aka sace suke.
A wani saƙo da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya wallafa, ya ruwaito gwamna Masari ya ƙara da cewa Shugaba Buhari ya damu ƙwarai kan yadda za a ceto ɗaliban, yana mai cewa ya dace ya ziyarci shugaban ƙasar ne kawai don ba shi ƙarin bayani kan halin da ake ciki na ceton.
A wannan rana ne kuma 'Yan daba suka tarwatsa taron matasan Arewa a Kaduna

Asalin hoton, CNG
A dai wannan rana ne kuma wasu tsageru da ake zargin 'yan daba ne sun tarwatsa taron gamayyar ƙungiyoyin Arewa Coalition of Northern Groups (CNG) a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna.
Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da suke tsaka da taron ƙara wa juna sani game da matsalolin tsaro da ke addabar yankin arewacin Najeriya.
Nastura Ashiru Shariff, jigo a ƙungiyar CNG, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.
Talata: Boko Haram ta ɗauki alhakin sace ɗaliban makarantar

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata 15 ga watan Disamba ne hantar iyayen ɗaliban sakandiren kimiyya ta Ƙanƙara ta fi kaɗawa tun bayan sace ƴaƴansu 333, da aka yi, domin a ranar ne ƙungiyar Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Abubakar Shekau ta bayyana cewa ita ce ta sace yaran nasu.
Saƙon da shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya fitar na tsawon minti 4:30, ya zo bayan kwana uku da sace ɗaliban su fiye da 500 abin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar baki ɗaya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriyar ta ce 'ƴan fashin da suka sace ɗaliban makarantar sakandaren kimiyyar ta Ƙanƙara sun tuntuɓi hukuma kuma tuni an fara tattaunawa kan abin da ya shafi tsaron yara da yadda za a mayar da su gida lafiya.
Tun da fari hukumomi sun ɗora alhakin sace ɗaliban kan 'yan bindiga.
Laraba: Za a fara rufe layukan waɗanda ba su yi rijista da lambarsu ta ɗan ƙasa ba

Asalin hoton, Google
A ranar laraba 15 ga watan Disamba ne dai hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC ta bayar da umarnin rufe duk wani layin waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN ba ko da tsoho ne.
Hukumar ta bayar da wa'adin makonni biyu ga masu layin waya waɗanda ke da wannan lambar ta NIN da su kai ta ga kamfanonin sadarwar da suke da rajista da su domin a yi musu rajistar lambar da layin wayarsu.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta bayar da umarnin sayarwa ko rajistar da sabbin layin waya a ƙasar.
Ga wasu daga cikin matakan da hukumar ta ɗauka domin tabbatar da wannan dokar:
- Tabbatar da cewa duka kamfanonin sadarwa sun bi umarnin farko na dakatar da rajistar sabon layin waya
- Kamfanonin sadarwa su buƙaci duka masu amfani da layukansu su bayar da sahihiyar lambar shaidar ta NIN domin haɗa ta da layinsu
- An bai wa masu amfani da layukan waya wa'adin mako biyu su kai lambar NIN ɗinsu (daga 16 ga watan Disamban 2020 zuwa 30 ga watan Disamban 2020)
- Duka layukan wayar da ba a yi musu rajista da lambar NIN ba nan da mao biyu za a rufe su
- Kwamiti na musamman ciki har da minista da wasu manya za su kasance masu sa ido domin tabbatar da kamfanonin sadarwa sun bi wannan umarni
- Karya wannan doka za ta jawo a ɗauki mataki, ciki har da yiwuwar ƙwace lasisin kamfani
Alhamis: Boko Haram ta fitar da bidiyon ɗaliban sakandiren Ƙanƙara da ke hannunta

Asalin hoton, BOKO HARAM
A ranar Alhamis 17 ga watan Disamba ne ƙungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon ɗaliban sakandiren Ƙanƙara da ta yi iƙirarin yin awon gaba da su ranar Juma'ar da ta wuce.
Bidiyon, wanda jaridar intanet ta HumAngle ta fara wallafawa, ya nuna ɗaya daga cikin ɗaliban yana roƙon gwamnatin Najeriya ta janye sojojin da ta aika domin ceto su yana mai cewa "babu abin da za su iya yi musu wallahi."
A cikin bidiyon mai tsawon minti shida da daƙiƙa 30, wanda ita ma BBC ta samu, ɗalibin ya nemi gwamnati ta rufe dukkan makarantu idan ban da makarantun Islamiyya da kuma "duk wata ƙungiyar ƙato-da-gora."
Akasarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun rufe makarantu
Kusan ana iya cewa al'ummar Najeriya sun shiga zulumi da zaman fargaba da kuma rashin tabbas tun bayan sace dalibai maza sama da 500 a makarantar sakandiren Ƙanƙara da ke jihar Katsina.
Boko Haram ta dauki alhakin yin garkuwa da daliban, ko da yake har yanzu ba a ji komai daga ɓangaren hukumomin Najeriya kan saƙon muryar da ƙungiyar masu tayar da ƙayar bayan ta fitar ba.
Wannan yanayi na matsalar tsaro ga alama ta sa wasu jihohin arewacin ƙasar ɗaukar matakin rufe makarantunsu.
Jihar Katsina ce ta fara rufe nata makarantun, sai Zamfara ta sanar da irin wannan mataki kan makarantu bakwai a yankunan da ke da iyaka da jihohin Katsina da Kaduna da kuma Sokoto.
Jihohi kamar Jigawa da Kaduna, su ma sun sanar da rufe makarantu, amma sun ce sun yi hakan ne saboda annobar korona.
Jihar Kano ta biyo baya inda a daren Talata ta sanar da rufe makarantun kwana sannan ta umarci iyaye su kwashe 'ya'yansu ba tare da bata lokaci ba. Lamarin dai ya zo ne kwana biyar, bayan sace ɗaruruwan ɗalibai a garin Ƙanƙara.
Juma'a: An ceto ɗaliban GSS Kankara

Asalin hoton, Reuters
A ranar Jumma'a ne gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce an samu nasarar karɓo yaran makarantar sakandaren Kankara su 344 a ranar Alhamis da daddare.
Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce a yanzu haka ana hanyar kai yaran birnin Katsina daga garin Tsafe na jihar Zamfara da ke maƙwabtaka da ita.
Kafin cetosu, ƙungiyar Boko Haram ta ce ita ta ɗauke su.
A cikin bidiyon, wanda jaridar intanet ta HumAngle ta fara wallafawa, ya nuna ɗaya daga cikin ɗaliban yana roƙon gwamnatin Najeriya da ta janye sojojin da ta aika domin ceto su yana mai cewa "babu abin da za su iya yi musu wallahi.
Garba Shehu ya nemi afuwa kan cewa ɗalibai 10 aka sace

Asalin hoton, BBC Hausa
Jim kaɗn bayan ceto su a wannan rana, sai mai taimakawa shugaban Najeriya kan harakokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya nemi afuwa kan bayanin da ya bayar cewa ɗalibai 10 ne kawai aka sace a makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina.
"Ina neman afuwa kan kuskuren bayanai da aka gabatar cewa dalibai 10 ne aka sace a makarantar kimiya ta Kankara.
"Wani ne wanda ya kamata ace ya sani ya bayar da bayanan kan adadin ɗaliban. Adadin kuma yanzu ya ci karo da waɗanda aka gani.
"Don Allah a fahimci cewa bayanan ba an bayar da su ba ne domin rage muhimmancin yanayin da aka shiga," in ji Garba Shehu.
Asabar: An yi garkuwa da mutum 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Assabar ne aka samu labarin cewa aƙalla matafiya 35 ne aka yi garkuwa da su ranar Juma'a a kan babbar hanyar Damaturu zuwa birnin Maiduguri.
Majiyoyin tsaro sun faɗa wa TheCable cewa 'yan bindigar da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka wa rukunin matafiyan a kusa da garin Kondiri da ke Jakana da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.
'Yan bindigar waɗanda suka bayyana cikin kakin sojoji, an ce sun saka shingen duba ababen hawa a kan babbar hanyar, inda suka yi awon gaba da fasinjojin a motoci ƙirar Hilux.
"Da farko fasinjojin sun hango hayaƙin taya amma sai suka zaci daji ake ƙonawa ba tare da sun fahimci cewa motar Dangote ba ce, wadda 'yan bindigar suka tare kuma suka cinna wa wuta," kamar yadda wata majiya ta shaida wa TheCable.
"Akasarin fasinjojin sun fantsama daji, an kama 35 daga cikinsu sannan an ƙona wasu motoci ƙanana biyu da kuma ta ɗaukar kaya. Motocin fasinja guda tara aka bari a kan titi, an wawashe dukkanin kayan da suka bari."
Wani babban jami'in ɗan sanda ya ce an ceto mutum 10 daga cikinsu, yayin da aka kai waɗanda suka ji rauni Asibitin Ƙwararru na Maiduguri domin duba su.
Matashiya ta kashe mutum uku da bam a Jihar Borno

Asalin hoton, NPSF
Har ila yau a wannan rana ne wata matashiya ta kashe mutum uku tare da jikkata biyu bayan ta tarwatsa kanta a taron jama'a a garin Konduga da ke Jihar Bornon Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wasu majiyoyin agaji da 'yan sa-kai na cewa lamarin ya faru ne a ranar ta Asabar.
"Mun ɗebe gawar mutum uku da kuma mutum biyu da suka ji manyan raunuka daga wurin," a cewar wani ma'aikacin agaji.
Wadda ta kai harin ta tayar da abin fashewar da ke jikinta a tsakiyar wasu mutane da ke shaƙatawa a kusa da gidan mai unguwa, a cewar wani shugaban ƙungiyar 'yan sa-kai.
Garin Konduga na da nisan kilomita 38 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, sai dai ya yi kama da irin wanda Boko Haram ta sha kaiwa ta hanyar amfani da ƙananan yara yayin taron jama'a.











